✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shugaba da Magatakardan Majalisar Neja sun kamu da COVID-19

Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Honarabul Bawa Wuse da kuma magatakardan majalisar, Mohammed Kagara sun killace kansu bayan kamuwa da cutar Covid-19. An gano cewa…

Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Honarabul Bawa Wuse da kuma magatakardan majalisar, Mohammed Kagara sun killace kansu bayan kamuwa da cutar Covid-19.

An gano cewa ‘yar Majalisar da ke wakiltar Gurara, Binta Mamman, ta kamu da cutar wanda hakan ne yasa ragowar ‘yan majalisar yin gwajin cutar.

Rahotanni sun bayyana cewa da yawa daga cikin ‘yan majalisar ta jihar Neja sun killace kansu kamar yadda mahukuntan lafiya suka shar’anta.

Majiya daga Majalisar, ta ce da yawa daga cikin wanda aka yi wa gwajin ba su harbu da cutar ba, face kakakin majalisar da kuma magatakardar majalisar.

Majiyar ta ce bayan killace kansu da suka yi, ana ci gaba da kula da su kamar yadda Hukumar NCDC mai kula da dakile cututtuka masu yaduwar a Najeriya ta tanadar.

A yayin da likafar cutar ke ci gaba a baya-bayan nan, ta harbi mutane da yawa, wanda har ta yi sanadiyar ajalin tsohon shugaban ma’aikatan jihar a ranar Asabar.

Ya zuwa yanzu, mutane da dama sun shiga fargaba dangane da cutar musamman wanda suka yi hulda da wasu daga cikin ‘yan majalisun jihar.

Bayan ba da umarnin rufe makarantu da gwamnatin jihar ta Neja ta yi, ta sake ba wa ma’aikata umarnin yin aikin daga gida daga ranar Litinin mai zuwa.