✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kada ya yi kalaci da yaro mai shekara 8 yana tsaka da wanka

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da yaron da dan uwansa suke tsaka da wanka a ruwan

Jami’an tsaro a yankin Kalimantan na kasar Indonesia sun tabbatar da rasuwar wani yaro mai kimanin shekaru takwas a duniya bayan da wata Kada ta cinye shi a lokacin da yake wanka a wani rafi.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da yaron da dan uwansa suke tsaka da wanka a ruwan, yayin da mahaifinsu kuma yake gida, kamar yadda Hukumar Bincike ta kasar, Oktavianto ta sanar.

Yayin da mahaifin yaron ya hangi kadar na kokarin cinye dan nasa, ya yi sauri ya fada ruwan da nufin ceto shi, amma tuni kadar ta riga ta tsere da shi cikin ruwan.

Daga nan ne kuma ya bi ta da duka amma duk da haka hakarsa ta gaza kai ga cimma ruwa.

A ranar Alhamis, jami’an tsaro suka sami wata kada a bakin ruwa mai kimanin tsayin inci shida, kuma aka samu gawar yaron a cikinta.

Jami’an tsaro sun saka wani bidiyo a YouTube inda suka nuna yadda aka ciro gawar yaron daga cikin kadar.