✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Joe Biden ya nada sabon Jakadan Amurka a Najeriya

Fadar White House ce ta sanar da nadin nasa ranar Litinin

Shugaban Amurka, Joe Biden, ya nada Richard Mills Jr a matsayin sabon Jakadan Amurka a Najeriya.

Sanarwar nadin nasa na kunshe ne a cikin wata wasika da Fadar Shugaban Amurka ta White House ta fitar ranar Litinin.

Sanarwar ta ce Mista Richard zai kasance daya daga cikin manyan jami’an da za su yi aiki a gwamnatin ta Shugaba Biden.

Kafin nadin nasa dai, sabon Jakadan shi ne Mataimakin Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya kuma gogaggen jami’in huldar diflomasiyya ne da ya yi aiki a matakai daban-daban.

A baya, ya taba zama Jakadan kasar a Armeniya, da kuma mataimakin Jakada a kasar Kanada.

Bugu da kari, jami’in ya yi aiki a matsayin mataimakin Jakada a birnin Beirut da ke kasar Lebanon da kuma mataimakin Jakadan a birnin Valetta na kasar Malta.

Sabon Jakadan na Najeriya dai dan asalin jihar Louisiana ne da ke Amurka, kuma kafin ya fara aikin jakadancin, kwararren lauya ne a birnin Washington D.C.