✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihohi hudu da aka samu karin mutum 40 sabbin kamuwa da Coronavirus

Muna tunatar da musulmi da su ci gaba da kiyaye matakan kariya a wannan lokaci na watan Azumi.

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka a Najeriya NCDC, ta sanar da samun karin mutum 44 sabbin kamuwa da cutar Coronavirus a Najeriya.

Ya zuwa ranar Litinin, NCDC ta ce cutar ta harbi mutum 163,837 tun bayan bullarta karon farko a watan Fabrairu.

NCDC ta ce cikin sa’a 24 da ta gabata, an samu mutum daya da cutar ta yi ajalinsa, inda jimillar adadin wadanda suka riga mu gidan gaskiya sanadiyar cutar suka kai 2,061.

Sabbin kamuwar da aka samu sun fito ne daga wasu jihohi hudu na kasar da kuma birnin Tarayya Abuja kamar haka; Enugu – 22, Legas – 15, Abuja – 4, Osun – 2, da Kaduna – 1.

Hukumar tana kuma tunatar da al’ummar musulmi da su ci gaba da kiyaye matakan dakile yaduwar cutar musamman yayin gudanar da ibadunsu a wannan lokaci na watan Azumi.

Ta ce, “A rika sanya takunkumin rufe fuska, bayar da tazara da wanke hannaye a kai a kai, sannan a guji shiga taron jam’a,” a shawarar da NCDC ta bayar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, daga ranar 5 zuwa 12 ga watan Afrilun bana, an yi wa mutum 34,997 gwajin cutar Coronavirus a fadin Najeriya.

Haka kuma, alkaluman NCDC sun nuna cewa, mutum 1,803,177 aka yi wa gwajin cutar tun bayan sanar da bullarta karon farko a ranar 27 ta watan Fabrairun 2020.