✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jihar Kaduna ta bukaci a kara mata kujerun Aikin Hajji 500

Jihar ce dai dama aka ba kujeru mafi yawa a Najeriya a bana

A daidai lokacin da ake ci gaba da kokawa a kan tsadar kudin kujerar Aikin Hajji, Jihar Kaduna, wacce aka ba kujeru mafi yawa a bana, ta bukaci a kara mata guda 500.

Shugaban Hukumar jindadin Alhazai ta Jihar, Dokta Yusuf Yakubu Alrigasiyyu ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a Kaduna, ranar Talata.

Ya ce sun aike da bukatar ce saboda su ba dimbin mutanen da suke son biyan kudadensu a Jihar yin hakan.

Idan za a iya tunawa, Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta ware wa Jihar kujeru 5,987 daga cikin adadin da Saudiyya ta ba Najeriya a bana, kuma ana sa ran kowannensu zai biya Naira miliyan 2 da dubu 900.

Ya kuma ce duk maniyyacin da ya biya kudin, za a ba shi kudin guzuri har Dalar Amurka 800.

Shugaban ya kuma bayyana dalilai da dama a matsayin wadanda suka haifar da karin kudin kujerar a bana da suka hada da tsadar masauki a kasar Saudiyya da tsadar farashin canjin Dala da ta man jirgi da kuma karin harajin VAT da Saudiyya ta yi zuwa kaso 15 cikin 100.

Sai dai ya ce duk da karin da aka yi na bana, kudin kujera a Najeriya na daya daga cikin wadanda suka fi arha a fadin duniya.

Dokta Yusuf ya ce akwai kasashe irin su Malaysia da Pakistan da Ghana da kuma Jamhuriyar Nijar da ke biyan kudade sama da na Najeriya.

Ya kuma yaba wa shugabancin hukumar NAHCON saboda tabbatar da cewa duk da wadamcan dalilan, kudin kujerar baoi ma kai Naira miliyan uku ba.