✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin wasannin farko na gasar Firimiyar Ingila a kaka mai zuwa

Ga jerin wasannin farko na gasar Firimiyar Ingila na kakar 2021/2022.

Hukumar Gudanarwar Gasar Firimiyar Ingila, ta fidda jadawalin wasanni gasar na kakar 2021/2022, inda ta ce za a fara wasannin farko a ranar 14 ga watan Agustan bana.

A wasu daga cikin wasannin farko, Tottenham da Manchester City za su barje gumi, sai kuma Brentford wadda a karon farko za ta buga gasar Premier League za ta karbi bakuncin Arsenal.

Sanarwar ta ce kungiyoyin Premier League za su iya buga wasanni tare da ’yan kallo a cikin fili, sai dai har yanzu ba a kai ga bayyana adadin ’yan kallo da za su shiga wasannin farko ba.

Kazalika, hukumar da ke shirya gasar ta ce tana ci gaba da fafutika ganin filayen wasa sun cika makil da ’yan kallo, kamar yadda aka saba ganin kafin bullar annobar Coronavirus.

Ga jerin wasannin farko na gasar Firimiyar Ingila na kakar 2021/2022:

  • Brentford da Arsenal
  • Burnley da Brighton
  • Chelsea da Crystal Palace
  • Everton da Southampton
  • Leicester City da Wolverhampton
  • Manchester United da Leeds United
  • Newcastle United da West Ham United
  • Norwich City da Liverpool
  • Tottenham Hotspur da Manchester City
  • Watford da Aston Villa