✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jerin shugabannin Amurka 10 da suka gaza tazarce

Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ki mika wuya kan sakamakon zaben Shugaban Kasar da aka gudanar a ranar 2 ga watan Nuwamba,…

Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ki mika wuya kan sakamakon zaben Shugaban Kasar da aka gudanar a ranar 2 ga watan Nuwamba, amma ta masu iya magana ce cewa ta faru ta kare.

Alkaluman sakamakon zaben sun riga sun nuna tsohon Mataimakin Shugaban Kasar Joe Biden ya riga ya kayar da Trump don zama Shugaban Kasar Amurka na 46.

Da wannan Shugaba Trump ya shiga kundin tarihi na shugabannin kasar da suka yi mulkin wa’adi daya kawai – suka gaza yin tazarce bayan wa’adi guda, saboda sun sha kaye a zabe.

Wadansu daga shugabannin da suka yi wa’adi daya suka gaza samun damar komawa gadon mulki sun hada da Shugaba John Tyler, wanda ya haye kujerar bayan rasuwar Shugaba William Henry Harrison kafin gabanin ya fadi zaben wa’adi na biyu ba ya cikin lissafin.

Haka Shugaba Lyndon B. Johnson wanda ya ki tsayawa takarar wa’adi na biyu a 1968, ban da shi sai shugabanni uku – James K. Polk da James Buchanan da Rutherford B. Hayes  wadanda suka yi alkawarin yin wa’adi daidaya kuma suka cika.

Trump ya shiga jerin shugabanni tara da suka gaza samun wa’adi na biyu ne bayan da Amurkawa suka ki zabarsu.

Shugabannin da suka nemi tazarce Amurkawa suka ki sun hada da:

John Adams, 1797-1801

Shi ne Shugaban Amurka na biyu kuma na farko da ya fadi zaben neman wa’adi na biyu.

Amurkawa na tuna wa da shi a matsayin daya daga cikin wadanda suka kafa kasar, amma batutuwa da dama sun dabaibaye mulkinsa da suka hada da rikici a tsakanin Sakataren Baitul Malin Kasar na lokacin Aledander  Hamilton da Mataimakin Shugaban Kasa, Thomas Jefferson.

Sai rikicin manoma masu magana da harsunan Jamusanci da Faransanci.

A zaben Shugaban Kasar na shekarar 1800 ya zo na uku bayan Jefferson da Aaron Burr.

John Quincy Adams, 1825-1829

Sai bayan shekara 25 aka sake samun Shugaban da ya fadi zaben wa’adi na biyu.

Abin mamaki, shi ne sa’ar da tarihin ya maimaita kansa shi ne kan dan tsohon Shugaba John Adams, wato John Quincy Adams.

Ya zama daya daga cikin shugabannin da suka mulki kasar masu hazaka kasancewar ya taba zama Sanata da jami’in diflomasiyya da Sakataren Wajen Kasar.

Amma yanayin da ya zama Shugaban Kasar ya shafi mulkinsa: ya zo na biyu a zaben, don haka aka ba majalisar kasar wuka da nama ta yanke hukunci.

Shugaban Majalisar Dokokin Kasar, Henry Clay, shi ne ya zaman na hudu a zaben – sai ya mara baya ga Adams, inda Adams ya zama Shugaban Kasa.

Shi kuma Clay ya zama Sakataren Wajen gwamnatinsa. Wanda ya zo na daya a zaben, Andrew Jackson, bai ji dadin “tsarin marar tsabtan nan ba” inda ya kashe shekara hudun mulkin Adams din wajen cin galabarsa a zabubbukan gaba, kuma ya yi nasarar haka.

Martin Van Buren, 1837-1841

Martin Van Buren ya yi aiki cikin ladabi da biyayya a lokacin mulkin Jackson na shekara takwas, farko a matsayin Sakataren Wajen Kasar, sai kuma Mataimakin Shugaban Kasa.

Shi aka zaba ya gaji mai gidansa Jackson a 1837 sai dai ya gamu da rashin sa’a, inda tattalin arziki ya karye watanni kadan da kama mulkinsa.

Kusan ya gaji matsalar daga mulkin mai gidansa – Andrew Jackson – sa’annan duk kokarin Martin Van Buren na kyautata lamarin sai ya zama tamkar yana magani kai na dada kaba.

Shekara hudu bayan nan sai William Henry Harrison ya yi masa kaye a zabe.

Franklin Pierce, 1853-1857

Sai kuma Shugaba Franklin Pierce wanda kusan za a iya cewa ba ya da wata sanayya daga masu zabe lokacin da aka zabe shi a 1852.

Wasu batutuwa da suka faru gabanin Yakin Basasar kasar a lokacin mulkinsa sun taka rawa wajen hana jam’iyyarsa sake tsayar da shi takara a wa’adi na biyu inda ta bai wa wani takarar.

Benjamin Harrison, 1889-1893

Benjamin Harrison shi ne na farko da ya fadi zabe a kuri’un gama-gari amma ya zama Shugaban Kasa ta hanyar kuri’un wakilai masu zabe (Electoral College), inda ya doke Shugaba mai ci Grover Cleveland.

Batutuwan haraji da na kasuwanci sun dabaibaye mulkinsa; bayan shekara hudu ya sha kaye a hannun Cleveland, hakan ya sa shi zama Shugaba na farko da ya yi hannun karba hannun mayarwa – a hannun shugaba Cleveland.

William Howard Taft, 1909-1913

Shugaba Teddy Roosevelt ne ya dauko William Howard Taft domin takarar wanda kwararre ne ta fuskar sanin shugabanci ya kuma samu yabo sosai daga hukumomin kasar, sai dai wani tsagin ’yan rajin kawo sauyi na Jam’iyyar Republican sun saka kafar wando daya da shi.

A takaice sai da ta kai, tsohon mai gidansa, Roosevelt ya kafa sabuwar Jam’iyyar Rajin Ci gaba inda ya yi takara da shi a 1912.

Sai dai ba wanda ya yi nasara a cikinsu inda daga baya Taft ya zama Babban Jojin Amurka, wanda ya ce ya ma fi son mukamin fiye da na Shugaban Kasa.

Ya taba rubuta cewa, “Ba na ma tuna cewa na taba zama Shugaban Kasa.”

Herbert Hoover, 1929-1933

Herbert Hoover ana masa ganin wanda ya shiga jerin shugabannin da aka taba samu mafiya munin tarihi.

Kasuwar shunku ta ruguje wata bakwai da hawa mulkinsa, wanda hakan ya janyo Gagarumin Mashassharar Tattalin Arziki a kasar.

Shi ma kamar Shugaba Van Buren, matsalar ba ta faro lokacinsa ba, amma yadda ya tunkari lamarin da rashin kwarewa ya kara ta’azzara lamarin.

Lokacin da aka kayar da shi, saboda miliyoyin Amurkawa sun zama ba su da muhalli sakamakon karayar tattalin arziki inda suka koma zama a kufai.

Jimmy Carter, 1977-1981

Duk da wa’adi guda kawai ya yi, babu wanda ya rayu tsawon lokaci bayan sauka daga karaga kamar Jimmy Carter, wanda har yanzu yana nan da rai.

Mai shekara 96 shi ne tsohon Shugaba mafi tsawon rai a Amurka inda ya shafe kusan shekara 40 bayan saukarsa daga mulki.

Shugabancinsa ya yi fama da matsalolin tattalin arziki da  rikicin garkuwa da Amurkawa da aka yi a Iran; rayuwarsa bayan mulki ta koma ayyukan kare hakkin dan Adam da diflomasiyya da yaki da talauci.

Ya wallafa wake-wake ya kuma shirya sako wadanda aka yi garkuwa da su a Koriya ta Arewa; sa’annan an ba shi Lambar Yabo ta Zaman Lafiya ta Nobel.

George H.W. Bush, 1989-1993

Shugabancinsa ya shaida faduwar katangar Berlin da kawo karshen Yakin Cacar Baka; sa’annan bayan galabar yaki cikin hanzari a Yakin Tekun Pasha a 1991, Bush ya samu amincewa da kashi 89 a ra’ayin jama’a.

Amma shekara guda bayan nan, lokacin da komadar tattalin arziki ta fara shafar Amurkawa, Bush ya rasa mulki a fadar White House a hannun Bill Clinton.

Ya rayu tsawon lokaci bayan saukarsa daga mulki kafin rasuwarsa a 2018, lokacin da yake raye ya kasance yana hada kai da sauran tsoffin shugabanni wajen ayyukan jin kai kamar agajin tsunami.