✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’ar Tarayya da ke Kashere Ta Rantsar Da bbin Dalibai 3,849

Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe ta rantsar da sabbin dalibai 3,849 a zangon karatu na shekarar 2022/2023. Shugaban Jami’ar, Farfesa Umaru Pate,…

Jami’ar Tarayya da ke Kashere a Jihar Gombe ta rantsar da sabbin dalibai 3,849 a zangon karatu na shekarar 2022/2023.

Shugaban Jami’ar, Farfesa Umaru Pate, ya ce wannan shi ne rantsar da sababbin Dalibai karo na 13 da Jami’ar ta yi.

Farfesa Pate, ya ce daliban da jami’ar ta dauka sun kusa rabin daliban da suka zabi yin karatu a jami’ar a matsayin zabinsu na farko ta hannun Hukumar JAMB.

Ya ce daliban sun kunshi ’yan Tsangayar Aikin Gona 131, Tsangayar Ilimi 698, Tsangayar Jinkai 258 sai Tsangayar Kimiyyar Rayuwa 1,058. Tsangayar Kimiyyar Mulki na da dalibai Sciences 428 sai Tsangayar Kimiyya da ke dalibai 1,276.

A cewarsa, daukacin daliban kammala rijistarsu ta shiga jami’ar kammala tantance su don zama cikakkun dalibai kafin bikin rantsuwar.

Ya sa sun dauki matakan da suka dace wajen shawo kan kalubalen dakunan kwana ga sababbin daliban.

“Aikin manyan gine-ginen dakunan kwanan daliban yana ci gaba da gudana sannan muna kwaskwarimar wasu a harabar jami’ar ta wucin gadi,” inji Pate

Ya kara da cewa akwai Darusa guda bakwai da jami’ar ta fara su a shekarar 2021 yanzu suna daf da samu cikakkiyar rijista wato accreditation daga hukumar da ke kula da jami’oi ta kasa NUC.

Ya kuma gargadi daliban da cewa jami’ar ba za ta lamunci shaye-shayen miyagun kwayoyi ko satar jarrabawa ko shiga kungiyar asiri ko yada labaran karya da sauran laifukan da suka saba dokokinta.