Danmajen Daura Alhaji Muhammadu Kabir ya bayyana gina Jami’ar Sufuri ta Kasa da za a yi a garin Daura da ke Jihar Katsina da cewa ci gaba ne ga Arewa ne baki daya ba Daura ko Jihar Katsina kadai ba.
Danmajen Daura Alhaji Kabir ne ya fadi haka a yayin da yake zantawa da Aminiya, inda ya ce “Mu yanzu al’ummar Masarautar Daura da shiyyar Daurar da Jihar Katsina baki daya, babu abin da za mu yi sai addu’a domin an share wa al’ummar wannan yanki hawayen shekara da shekaru kan rashin samun wasu muhimman abubuwa na gwamnati lura da irin tarihin da wannan sashe yake da shi. Sannan wadannan wurare uku da gwamnatin ke shirin yi wanda muka fara ganin na farko. Wato Jami’ar Sufuri da Kwalejin Kimiyya da Sana’a ta Tarayya da kuma Asibitin Tarayya duk abubuwan ci gaba ne.”
Danmajen ya ce da an fara aikin gina wannan jami’a za a fara samun habakar tattalin arzikin al’ummar yankin musamman masu kananan sana’o’i.
“Aikin jami’ar ya kara tabbatar mana da batun hanyar jirgin kasa da ake maganar za a yi a wannan shiyyar. Sai mu ce muna godiya, musamman ga Gwamna Aminu Bello Masari wanda ya bayar da filaye da duk wata gudunmawa da goyon baya don ganin an aiwatar da wadannan ayyuka na raya kasa da ci gaban al’umma. Su ma sarakunan Katsina da Daura sun bayar da gagarumar gudunmawa wajen ganin tabbatuwar wadannan ayyuka. Shi kuwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari wanda ya kawo mana wadannan ayyukan ci gaba babu abin da za mu yi masa sai addu’ar Allah Ya sa ya gama jagorancin da yake kai lafiya,” inji shi.
Da ya juya kan al’ummar da wadannan ayyuka suka shafa musamman yankin Daura, ya ja hankalinsu cewa su bayar da dukkan gudunmawa da hadin kai domin a samu nasarar wadannan ayyuka, “Mu nuna halinmu na Daurawa wajen karrama baki da girmama su,” inji shi.