✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jami’an Gwamnatin Trump da suka yi murabus ana dab da saukarsa

Tuni dai ya ce ba zai halarci taron rantsar da sabuwar gwamnatin ba.

Nan da yan sa’o’i kadan Shugaba Donald Trump zai yi bankwana da Fadar White House bayan kammala wa’adinsa na mulki daya bayan ya sha kaye a zabe.

Trump zai mika gwamnati ne ba don ya so ba, ba kuma don ya yarda an kayar da shi a yunkurinsa na yin tazarce ba. Tuni dai ya ce ba zai halarci taron rantsar da sabuwar gwamnatin ba.

Kwana biyar kafin cikar wa’adin Mista Trump wanda ya sha kaye a hannun Mista Joe Biden a zaben, jami’an gwamnatinsa suka yi ta murabus daga mukamansu.

Sun fice daga gwamnatin mai cike da rudani ne don nuna fushinsu kan tunzura mutane da Trump ya yi suka yi kutse da tayar da hargitsi a zauren Majalisar Dokokin kasar yayin da take shirin bayar da shaidar nasarar zabe ga Biden da Matimakiyarsa Kamala Harris.

Ga kadan daga cikin jami’an gwamnatin Trump da suka ajiye mukamansu bayana hargitsin:

Chad Wolf

Wolf, Mukaddashin Sakataren (Minista) Tsaron Cikin Gida, ya yi murabus daga mukaminsa ne a ranar Litinin a shafin sada zumunta, ‘’yan kwanaki bayan ya nemi Shugaba Trump “cikin kakkausar murya ya yi tir da tashin hankalin da ya faru a majalisar.”

A wata wasika, Wolf ya ce ya yi niyyar aiki da gwamnatin zuwa karshen wa’adinta, amma ajiye aikinsa “ya samo tushe ne daga irin balahirar da ta faru kwanakin baya,” ciki har da “hukunce-hukunce marasa kan gado da kotuna suka yi” game da ikonsa a matsayin Mukaddashin Sakatare.

A watan Nuwamba, wani alkalin tarayya a New York ya yanke hukucin cewa ba ya da ikon takaita izinin aiki ga dubban daruruwan bakin da ba su da takardu da suka shigo kasar lokacin suna yara da aka fi sani da: ‘masu neman zama ’yan kasa.’

 

Elaine Chao

Chao, ita ce Sakatariyar (Ministan) Sufuri, kuma Sakatariyar farko a gwamnatin da ta yi murabus bayan hargitsin da aka yi a majalisar.

Cikin wasikar da ta aike wa abokan aikinta, Chao, wacce matar Shugaban Masu Rinjaye a Majalisar Dattawan Amurka Mitch McConnell, ta ba da hujjar ajiye mukaminta da yamutsi.

“Kasarmu ta ga mummunan yanayin da za a iya kauce wa faruwarsa yayin da magoya bayan Shugaba Trump suka yi wa majalisa tsinke bayan jawabin da ya yi a wani gangami,” Chao ta rubuta.

“Ina da tabbacin haka lamarin yake a wajen galibinku, na yi matukar kaduwa da lamarin ta yadda ba zan iya komawa gefe guda in zura ido ba.” Murabus dinta ya fara aiki ne tun ranar 11 ga Janairu.

 

Sakatariyar Ilimi Betsy DeVos

Sakatariyar Ilimi Betsy DeVos ta ajiye aikinta ranar Alhamis da daddare, inda ta zama ta biyu da ta ajiye aiki a Majalisar Ministocin Trump, bayan yamutsi a majalisar.

A takardar ajiye aiki ga Shugaba Trump, DeVos ta ce “Babu kuskure ko kadan idan aka ce kalamanka na tunzuri ne ummul haba’isin hargitsin, a gare ni su ne suka tunzura masu kutsen.

“Yara kanana a kasar nan wadanda ba su iya mayyaze komai na kallon abin mamakin da ya faru a majalisar,” ta kara da cewa, “kuma kowanenmu na da alhakin yin tunanin abin da ya dace wajen nuna misalin da za su kwaikwaya daga gare mu.”

 

Matthew Pottinger

Pottinger, Mataimakin Mai ba da Shawara kan Tsaron Kasa, Robert O’Brien, ya yi aiki da gwamnatin tun farkon farawarta, ya yi murabus ranar da aka yi yamutsin.

Ya kasance babban mashawarci kan kasar China wanda shi ne jigon samar da manufofin Trump kan gwamnatin Beijing.

“Matt Pottinger ya yi wa Amurka da gwamnatin Trump aiki bil hakki da gaskiya cikin shekara hudun da suka wuce,” kamar yadda O’Brien ya wallafa a shafin Tiwita inda ya tabbatar da ficewarsa daga gwamnatin.

“Aikinsa ya yi matukar ankarar da kasarmu da kuma duniya baki daya kan barazanar da Jam’iyyar Kwaminisanci ta China ke yi wa duniya.”

 

Sarah Matthews

Mataimakiyar Sakataren Watsa Labarai a fadar White House, ta ce a jawabin ajiye aikinta cewa “Na ji dadi da na yi aiki a gwamnatin Trump kuma ina alfahari da manufofin da muka samar.”

Amma “a matsayina na wadda ta yi aiki a zaurukan majalisar, na yi matukar kaduwa da abin da na gani. Zan sauka kawai, nan take,” inji Matthews: “Kasarmu tana bukatar mika mulki cikin lumana.”

 

Mick Mulbaney

Mulbaney, tsohon Mukaddashin Shugaban Ma’aikatan Trump ya ce ya ajiye aikinsa na Manzon Amurka na Musamman a Arewacin Ireland, kuma ya kira Sakataren Wajen Amurka, Mike Pompeo domin sanar da shi matakin nasa.

“Ba zan yi aikin ba. Ba zan tsaya ba,” inji Mulbaney, wanda ya ce ya yi magana da wadnsu jami’an gwamnatin Trump da ke tunanin ficewa daga cikinta.

“Ba mu yi rantsuwar aikin kan abin da kake tunani ba,” ya ci gaba da cewa.

“Mun shiga gwamnatin ce domin sake daga izzar Amurka; muna aiki ne domin sassauta haraji da saukaka dokoki.

“Shugaban yana da jerin abubuwan da ya cimma nasara a kansu wadanda za mu yi alfahari da su. Sai dai dukkansu sun shiririce a jiya-jiyan nan.”

Mulbaney ya ce ra’ayin Shugaba Trump ya sauya “kan yadda ya san shi wata takwas da suka wuce.”

Ya ce da dama daga cikin jami’an gwamnatin sun zabi ci gaba da rike mukamansu ne saboda tunanin idan suka ajiye aikin “mai yiwuwa Shugaban ya nada wanda ya fi muni a madadinsu” a ’yan kwanaki kalilan da suka rage masa a madufun iko.

 

Stephanie Grisham

Tsohuwar Sakatariyar Watsa Labarai a fadar White House, ta ajiye mukaminta na Shugabar Ma’aikatan Uwargidar Shugaban wato Melania Trump.

A wani sakon Twitter da ta sanar da ficewarta daga gwamnatin, Grisham ba ta bayyana ko hakan na da alaka da yadda Shugaban ya tunkari hatsaniyar ko a’a ba. Ba ta kuma ambaci sunan Shugaban ba.

“Abin alfahari ne gare ni na bauta wa kasata a fadar WhiteHouse,” kamar yadda ta rubuta. “Ina cike da alfaharin kasancewa a ofishin Uwargida Melania inda na tallafa wa yara a ko’ina kuma ina alfahari da dimbin nasarorin da gwamnatin nan ta samu.”

 

Anna Cristina ‘Rickie’ Niceta

Niceta ta yi aiki a matsayin Sakatariyar Jin Dadi a fadar White House kusan tun farkon gwamnatin Trump.

Kamar yadda CNN ta ruwaito, kafar da ta fara sanar da ficewarta daga gwamnatin, ayyukanta sun hada da lura da “dukkan abubuwan da ke gudana a fadar White House, kama daga kananan tarurruka a Shiyyar Yammacin Fadar har zuwa bukukuwan shekara-shekara na Easter Egg Roll da na Halloween da kuma ziyarar da shugabannin kasashe ke kai wa fadar da kuma tarurrukan majalisun dokokin kasar a cikin fadar.”

 

Tyler Goodspeed

Goodspeed,  Shugaban Majalisar Bayar da Shawara kan Tattalin Arziki ta gwamnatin Trump, ya fada wa wani dan jarida a New York washegarin ranar da aka yi kutse a Majalisar cewa: “Abubuwan da suka wakana a Majalisar Dokokin Amurka a jiya, sun sanya ni yanke shawarar cewa ba makawa in fice daga gwamnatin.”

 

Eric Dreiband

Dreiband, Mataimakin Antoni Janar kuma Shugaba a Bangaren Hakkokin Fararen Hula a Ma’aikatar Shari’ar Amurka, ya sanar da murabus dinsa cikin wani jawabi a ranar Alhamis, washegarin hargitsin.

Yanzu haka dai Sakataren Wajen Amurka Mike Pampeo ya sanar da janye shirinsa na kai ziyara kasashen Turai saboda kallon abin kunya da ake yi wa Amurka kan kutsen magoya bayan Trump ga majalisar.

Hargitsin da ya faru a Majalisar ya sa Majalisar Wakilan Amurka ta fara yunkurin tsige Shugaba Trump kan zarginsa da ingiza kutsen da magoya bayansa suka yi ga majalisar.

Kuma wakilan jami’yyarsa ta Republican sun nuna za su goyi bayan a tsige shi, idan aka kada kuri’ar haka.

A karshe dai, nan da ’yan sa’o’i za a rantsar da sabon Shugaban Amurka, Joe Biden da Mataimakiyarsa, Kamala Harris a wa’adin mulkinsu na farko.

Shugaba Trump wanda ya amince ya mika mulki ga sabon shugabancin kasar cikin lumana dai ya ce ba zai halarci taron bikin rantsarwar ba.

Trump na ikirarin cewa shi ne a ci zaben amma aka murde masa, duk da cewa dukkannin hukumomi da kotunan kasar sun tabbatar da an yi masa mummunan kaye.