✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

JAMB ta kara lokacin yin rajistar masu neman DE

Hukumar JAMB ta tsawaita lokacin yin rajista ga dalibai da ke neman gurabun karatu kai-tsaye da mako guda

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta tsawaita lokacin yin rajista ga dalibai da ke neman gurabun karatu kai-tsaye da mako guda.

JAMB ta tsawaita lokacin rajistar DE ne daga ranar Alhamis 20 ga watan Afrilu, 2023 da ta shirya rufewa da farko, zuwa ranar Juma’a 27 ga watan.

Mai magana da yawun JAMB, Farfesa Fabian Benjamin ya ce karin lokacin zai ba da dama ga dalibai masu takardar shaidar jarawabar “Cambridge A/Level da ba su yin rajista ba saboda matsalar tantance takardunsu a baya su damu damar yin rajista.

“Haka kuma sauran dalibai da ba su samu yin rajista ba da farko za su samu damar yin hakan a mako gudan da aka kara.”

Ya ce domin saukake tantance takardun Cambridge A/L, JAMB na aiki tare da Cibiyar Raya Al’adun Kasar Birtaniya (British Council), wadda za ta samar da shafin da JAMB za ta yi amfani da shi kai-tsaye wajen tantance takardun.

“Saboda haka duk mai takardar Cambridge da suke neman DE na iya zuwa ofisoshin JAMB mafi kusa da shi ya yi rajista,” in ji Farfesa Benjamin.

Sai dai ya bayyana cewa hakan bai shafi wadanda suka zana jarabawar Cambridge amma sakamakon jarawarsu ba ta riga ta fito ba.