✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Jakadan Najeriya a kasar Amurka ya rasu

Allah Ya yi wa Jakadan Najeriya a kasar Amurka, Mai Shari’a Sylvanus Adiewere Nsofor rasuwa. Jakadan na Najeriyan ya rasu ne yana da shekara 85…

Allah Ya yi wa Jakadan Najeriya a kasar Amurka, Mai Shari’a Sylvanus Adiewere Nsofor rasuwa.

Jakadan na Najeriyan ya rasu ne yana da shekara 85 a wani asibiti da ke yankin Maryland na kasar Amurka ranar Alhamis da dare.

A ranar 12 ga watan Nuwamban 2017 ne Mai Shari’a Sylvanus Nsofor ya fara aiki a matsayin Jakadan Najeriya a Amurka, har zuwa lokacin da ya koma ga Mahaliccinsa.

Ya samu mukamin ne bayan rasuwar tsohon Jakadan Najeriya a Amurka, Farfesa Adebowale Adefuye, wanda ya mutu dab da karewar wa’adinsa.

Mamacin shi tsohon Alkali ne a Kotun Daukaka Kara ta Najeriya.

An haife shi ne a ranar 17 ga Maris, 1935 a Oguta, Jihar Imo, kuma tsohon dalibin tsohuwar Kwalejin Aikin Lauya ta Holbor da ke birnin London na kasar Birtaniya ne.

A kwalejin ya samu digirinsa na farko a 1962 kafin ya samu digirinsa na biyu a 1964 daga Kwalejin Tattalin Arziki ta London.