✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

ISWAP ta kashe wani Babban Kwamandan Boko Haram a Borno

Wannan daya ce daga cikin gagarumar barnar da ISWAP ta yi wa Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Kungiyar ISWAP mai ikirarin jihadi a kasashen Yammacin Afirka, ta kashe wani babban Kwamandan Boko Haram da ake kira Ma Ummate, a wani hari na ramuwar gayya da ta kai wa mayakansa a Jihar Borno.

Wannan dai na zuwa ne a sakamakon wata mummunar arangama da aka yi tsakanin bangarorin mayakan biyu a yankunan Chinene da Barawa da ke Jihar Borno.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, marigayi Ma Ummate ya rike mukamin Gwamnan Boko Haram, kafin mayakan na ISWAP su kai masa wani hari na kwanton bauna wanda ya yi ajalinsa a tsaunin Mandara da ke Gabashin dajin Sambisa.

Da yake karin haske ranar Asabar a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno, wani mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya, Zagazola Makama, ya bayyana cewa; “Harin kwanton bauna na sa’o’i biyu da aka yi wa ayarin motocin Ma Ummate, ya yi sanadiyar kashe mayakan Boko Haram da dama a yankunan da ke iyaka da kasar Kamaru.”

Makama ya ce mayakan ISWAP da ke cikin manyan motoci bakwai da babura 10 sun yi galaba a kan ‘yan ta’addan na Boko Haram, inda suka samu nasarar harbin Ma Ummate a kahon zuci da wasu sassan jikinsa.

Ya kara da cewa ISWAP ta kuma kwace makaman Boko Haram da manyan motoci da babura da suke amfani da su wajen kai wa al’ummomi hari a yankunan da ke iyaka da kasar Kamaru.

A cewarsa, “wannan hari na kwanton bauna da kungiyar ISWAP ta kai ya zo ne bayan ’yan kwanaki da ita ma Boko Haram ta kashe wani kwamandan kungiyar ta su mai suna Abou Sadiqou Boorubouru da wasu mayakansu.

Don haka wannan hari da ISWAP ta kai hari ne ramuwar gayya,” a cewar Makama.

A halin da ake ciki, mayakan kungiyoyin ta’addan biyu sun dakatar da duk wasu manyan hare-hare da suke kai wa Sojojin Najeriya da sauran jami’an tsaro.

A cewarsa, ISWAP na mayar da hankali wajen tunkarar abokan hamayyarta domin kawar da dukkan mayakan Boko Haram a dajin Sambisa da yankin tafkin Chadi.

Kazalika, ya ce Ma Ummate wanda aka fi sani da Muhammad shi ne dan ta’adda na 271 a cikin jerin sunayen da sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo.

Ma Ummate dai ya shiga kungiyar Boko Haram a shekarar 2009 – kuma ya zama Khayd [Gwamna], a majalisar Marigayi Abubakar Shekau.

Babu wata masaniya game Ma Ummate wanda aka haifa a Mandara, har sai da ya shiga harin mamaye garin Bama a watan Satumban 2014, inda aka kashe daruruwan mutane.

Baya ga haka, sunansa ya kara fitowa fili bayan harin da aka yi garkuwa da mutane da dama har ta kai ga an ayyana Bama a matsayin daular Halifancin Musulunci ga Boko Haram a wancan lokacin.

“Ma Ummate dai ya shahara a cikin mayakan bayan ya jagoranci kashe mutane sama da 400 a gadar Bama, ya kuma daure mata sama da 3,000 bayan ya kashe mazajensu da dama a gidan yari na Bama.”

Zagazola ya kuma ce, kafin rasuwarsa, Ma Ummate ya jagoranci tawaga da dama wajen kai hari a sansanin sojoji ciki har da Konduga, Kawuri, Banki, Bama da Madagali a Jihar Adamawa.

Ya kuma bayar da gudunmawa wajen kai hare-haren da dama a Arewa maso Gabashin Borno da Adamawa.

A cewar Makama, kisan Ma Ummate za ta kasance daya daga cikin gagarumar barnar da ISWAP ta yi wa Boko Haram a Arewa maso Gabas.

Ya kuma bayyana cewa, lokacin da aka samu labarin kisan Ma Ummate, al’ummomin da ke daukacin garuruwan Bama, Gwoza da Banki hade da al’ummomin da ke kan iyakar Kamaru sun yi farin ciki matuka.