✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

ISWAP ta kashe Matafiya biyu a Borno

Akwai yiwuwar a samu karin salwantar rayuka sakamakon zubar da jini da wasu matafiyan ke yi babu kakkautawa.

Wasu matafiya biyu sun rasa rayukansu a safiyar Talata sakamakon wani hari da mayakan ISWAP suka kai kan hanyar Gamboru Ngala a Jihar Borno.

An bayyana cewa mutanen biyu da ’yan ta’addan suka harbe direbobi ne a cikin motocinsu yayin da suke kan hanyar Ngala tun kafin cikar wa’adin bude hanya sakamakon dokar takaita zirga-zirga da ke aiki a yankin.

Mayakan na ISWAP sun yi ruwan harsashai hadi da tayar da bama-bamai wanda ya bar wasu da suka samu munanan raunuka suna zubar jini mai yawa har zuwa lokacin da jami’an tsaro suka kawo musu dauki.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa harin ya faru ne a lokacin da wata motar tirela ta taka wasu bama-bamai da suka tashi, lamarin da ya yi ajalin direban tirelan nan take tare da raunata sauran mutanen da ke cikin motar.

Majiyar ta ce akwai yiwuwar a samu karin salwantar rayuka sakamakon zubar da jini da wasu matafiyan ke yi babu kakkautawa kafin kawo musu agaji.

Wata Majiyar soji ta ce, “Nan da nan bam din ya tashi, ‘yan ta’addan da suka yi dako a gefe suka shiga suka kwashe kayan abincin da ke cikin tirelar tare da lodawa a motocinsu kirar hilux guda biyu.

“Maharan sun kuma kama wata mota kirar Volkswagen Bus ta daukar kaya bayan sun kashe direban.  Daga nan sai suka nemi mata da yara da sauran fasinjojin da ke ciki da su sauka domin tafiya da motar zuwa cikin daji.

“Bayan kashe wadannan matafiya, sun kuma dakatar da wata tirela da ke dauke da karafa suna tunanin kayan abinci ne.  Da suka gano cewa ba kayan da ake amfani da su ba ne suka ba shi izinin tafiya.”

Majiyar sojin ta shaida wa Aminiya cewa “Direban da wadanda harin ya shafa sun ki mutunta dokar takaita zirga-zirga da aka saka a yankin.

“Hanyar yawanci tana budewa ne da karfe 8 na safe kuma a lokacin ne jami’an tsaro za su fara fara binciken ababen hawa da kuma yanayin hanyar don samar da tsaro ga matafiya.

“Sai dai wadannan direbobi da iftila’in ya afku a kansu sun yi gaggawar fita ne tun kafin a bude hanya.

Wakilinmu ya ruwaito cewa jami’an tsaro sun ziyarci wurin da lamarin ya faru inda suka kwashe wasu mata da suka jikkata da kuma gawarwakin direbobin biyu da suka mutu.