✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta yi wa Lebanon luguden bama-bamai

Isra'ila ta yi wa Lebanon kashedi kan hare-haren kungiyar Hezbollah.

Jiragen yakin Isra’ila sun yi wa kasar Lebanon luguden bama-bamai a cikin dare a matsayin ramuwar gayya kan rokokin da aka harba mata daga Lebanon a wannan makon.

Kasashen biyu masu makwabtaka da juna sun tabbatar da harin na ranar Laraba da dare, wanda Rundunar Sojin Isra’ila (IDF) ta ce jiragen yakinta ne suka kai a kan wuraren da aka harbo wa Isra’ila rokokin.

Isra’il ta zargi gwamnatin Lebanon da hannu a hare-haren, ta kuma yi kurari cewa ba za ta sassauta wa duk wani runkuri na keta huruminta a matsayin kasa ko kuma kai wa fararen hulan kasarta hari ba.

IDF ta ce jiragen sun kuma tarwatsa wuraren da aka yi amfani da su wurin kai wa Isra’ila a baya kafin na ranar Talata.

Harin na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Isra’il ke kokarin ganin ba a maimaita kazamin fadan da aka yi a yankin Zirin Gaza tsakanin kasar da mayakan kungiyar Falasdiwa ta Hamas ba.

A baya-bayan nan an harba rokoki daga Lebanon zuwa yankin Kudancin iyakar Isra’ila.

Hare-haren na zuwa ne yayin da Lebanon ke fama da rikice-rikicen tattalin arziki da na kudi da kuma siyasa da ya hana ta samun tsayayyiyar gwamnati na tsawon shekara guda.

Shugaban Lebanon, Michel Aoun ya ce hare-haren da Isra’ila ta kai kan kauyukan kasarsa “shi ne irinsa na farko tun 2006 kuma ya nuna muguwar niyya” kan Lebanon.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Mista Michel ya ce Lebanon za ta mika koke ga Majalisar Dinkin Duniya.