✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta saki Bafalasdine bayan ya shafe shekara 17 a daure

Shi ne dai Bafalasdine fursuna mafi dadewa a hannun Isra'ila

Kasar Isra’ila a ranar Litinin ta saki fursuna mafi dadewa a tarihi bayan ya shafe shekara 17 a tsare, bisa zargin safarar makamai, kamar yadda dansa ya tabbatar.

Wani Kakakin Kungiyar Fursunonin Falasdinawa ya ce an saki Fuad Shubaki, mai shekara 83, daga gidan yarin Ashkelon, kuma yanzu haka yana kan hanyarsa ta zuwa Ramallah da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan, kamar yadda Hazeem, dan Shubakin ya tabbatar.

Shubaki dai babban mamba ne a jam’iyyar Fatah ta tsohon Shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas.

Jami’an tsaron Falasdinu ne suka kama shi a shekara ta 2002, lokacin da ake tsaka da rikicin ‘Intifada’ a karo na biyu.

An dai zarge shi ne da safarar makaman daga kasar Iran zuwa yankin Zirin Gaza, a kan wani jirgin ruwa, yayin da Isra’ila ta kwace su a kusa da tekun Red Sea.

Sojojin Isra’ila dai a wancan lokacin sun yi zargin cewa yana dauke da tan 50 na makamai, ciki har da roket mai gajeren zango da na kakkabo makamai masu linzami da kuma wasu abubuwan fashewa da aka shigo da shi daga hannun kungiyar Hezbollah.

A shekarar ta 2002, hukumomin Falasdinu suka tsare shi, sannan suka ajiye shi a garin Jericho da ke Gabar Yammacin Kogin Jordan, karkashin kulawar Amurka da Birtaniya.

An dai yanke masa hukuncin daurin shekara 20, inda daga bisani aka rage wa’adin zuwa shekara 17.

AFP