✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Isra’ila ta kai wa jirgin ruwan Iran hari a teku

Ana zargin jirgin da zama cibiyar leken asiri ne da wadata ’yan tawayen Houthi makamai

Iran na zargin Isra’ila da kai wa jirgin ruwanta hari a Yemen a Bahar Maliya a yayin da ake kokarin cimma yarjejeniyar amfani da Nukiliya da Iran din.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta tabbatar a ranar Laraba cewa jirgin ruwan MV Saviz ya lalace sakamakon harin da aka kai masa a Bahar Maliya ranar Talata.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta ce, “harin ya lalata wani bangare na jirgin ruwan, amma an yi sa’a babu wanda ya samu rauni.”

Tun shekarar 2016 da jirgin ruwan dakon kayan ya fara zarya a tekun da ke kusa da Yemen, ake zargin amfani da shi a matsayin sansanin Sojojin Juyin Juya Hali na Iran (IRGC) da wadata ’yan tawayen Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran da makamai.

MV Saviz ya kuma yi kaurin suna a matsayin cibiyar leken asirin IRGC.

Ana zargin Isra’ila da hannu na kai harin, a yayin da wakilan Iran ke ganawa da Amurka a Vienna domin cimma yarjejeniyar Nukiliya.

Amurka ta ce Isra’ila ce ta kai harin

Gidan talabijin na kasar Iran, ya ambato wani rahoto a jaridar New York Times na kasar Amurka na zargin gwamnatin Isra’ila na sanar da Amurka cewa sojojinnta sun samu jirgin Iran din a ranar Talata.

Amukra ta ce harin da Isra’ila ta kai wa jirgin ruwan ramuwar gayya ce a kan harin da Iran ta taba kai w jirgin ruwan Israila; Sai dai Rundunar Sojin Amurka ta ce na ta d ahannu a kai harin.