✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Iran za ta karbi bakuncin tattaunawa kan makomar Afghanistan

Yayin taron, Iran za ta bukaci a kafa gwamnatin da kowa zai yi na’am da ita.

Kasar Iran ta ce ta kammala shirin karbar bakuncin tattaunawa a mako mai zuwa kan makomar siyasar kasar Afghanistan da kuma batun kafa sabuwar gwamnatinta.

Iran dai ta ce taron zai gudana ne a babban birninta wato Tehran.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar, Saeed Khatibzadeh a ranar Litinin ya ce, “Za a fara taron ne ranar 27 ga watan Oktoba, kuma zai samu halartar Ministocin Harkokin Wajen kasashen da ke da makwabtaka da kasar, da kuma wakilan kasar Rasha.”

Ya kara da cewa yayin taron, Iran za ta bukaci a kafa gwamnatin da dukkan bangarori, ciki har da Taliban za su yi na’am da ita.

 “Abin da Iran take bukata a Afghanistan shi ne zaman lafiya, ba tashin hankali ko ta’addanci ba.

“Saboda haka, dukkan makwabtan kasashe dole su goyi bayan mutanen Afghanistan,” inji kakakin na Ma’aikatar Iran, yayin wani taron manema labarai a birnin Tehran.

A kasar Iran dai, har yanzu akwai mabanbantan ra’ayoyi a kan hanyoyin da gwamnatin kasar ya kamata ta mu’amalanci gwamnatin Taliban a nan gaba, wacce ake wa kallon mai tsattsauran ra’ayi.

Yayin da wasu ke da ra’ayin cewa ’yan Taliban din sun canza kuma ba su da zafin akidar da aka sansu da ita a da, wasu kuwa na cewa abubuwan da suka faru a kasar a ’yan kwanakin nan sun nuna akasin hakan.

Mutanen dai na kallon cewa kasar Iran wacce ’yan Shi’a ke jagoranta za ta ci gaba da zama abokiyar gaba ga kasar Afghanistan wacce masu akidar Sunni ke jagoranta. (NAN)