✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPPIS: Gwamnati da malaman jami’a za su hau kan teburi

Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) game da mastalolinsu da bangarorin ke ta kullin kurciya a kai. Kakakin Ma’aikatar Kwadago…

Gwamnatin Tarayya za ta yi zama da Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) game da mastalolinsu da bangarorin ke ta kullin kurciya a kai.

Kakakin Ma’aikatar Kwadago da Samar da Ayyuka, Charles Akpan ya sanar da haka a cikin wani sako, sai dai bai bayyana batutuwan da zaman zai tattauna ba.

“Minista Chris Ngige zai yi zama da Kungiyar Malaman Jami’o’i ranar Alhamis 15 ga Oktoba, 2020”, inji sanarwar.

Wata majiya ta ce zaman zai tattauna da kan tsarin biyan albashin bai-daya na IPPIS da gwamnati ta ce wajibi ne malaman su shiga su kuma suka ce allambaran.

A ranar Talata, washegarin ganawar ASUU da Majalisar Tarayya,  gwamanti ta ce tana duba yiwuwar rungumar tsarin biyan albashi na UTAS da kungiyar ta gabatar.

Karin bayani na tafe….