✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

IPOB ta ba ’yan kabilar Ibo kwana 3 su binne gawarwakin da suke ajiye da su

Ta ce ta gano ajiya su na jawo wa yankin koma-baya

Haramtacciyar kungiyar nan mai fafutukar kafa kasar Biyafara ta IPOB, ta ba ilahirin mazauna yankin Kudu maso Gabas wa’adin kwana uku su binne gawarwakin ’yan uwansu da suke ajiye da su.

Kungiyar ta ba da umarnin ne ranar Laraba, a cikin wata sanarwa da Kakakinta, Emma Powerful ya fitar.

IPOB ta ce al’adar nan ta ajiye gawarwakin a dakunan adana su tsawon lokaci ita ce ummul-aba’isun tarin kalubalen da yankin ke fuskanta.

Kungiyar ta bukaci ’yan kabilar Ibo da su farfado da tsohuwar al’adarsu ta binne gawarwaki, in kuwa ba haka ba, za ta tilasta kulle ilahirin dakunan adana gawarwakin da ke yankin.

Sanarwar ta ce, “Kungiyar IPOB mai daraja, karkashin jagorancin babban kwamnadanta, Mazi  Nnamdi Okwuchukwu Kanu, tana sanar da dukkan ’yan Biyafara, abokai da masoyansu cewa lokaci ya yi da za su fara binne gawarwakinsu nan da kwana uku kamar yadda ake yi zamanin iyaye da kakanni.

“IPOB ta zurfafa bincike, inda ta gano cewa yawan ajiye gawarwaki tsawon lokaci na daya daga cikin abubuwan da ke jawo wa yankinmu tarin kalubale.

“Magabatanmu na binne gawarwakin matattunsu cikin kwana uku da mutuwarsu, wannan ita ce al’adarmu tun tale-tale saboda tana taimaka wa magabatan namu a gargajiyance.

“’Yan kabilar Ibo mutane ne masu kyakkyawar al’ada wacce magabatanmu suka yi kokarin alkinta ta, tun shekaru aru-aru.

“Sabuwar al’adar da mutanenmu suka tsiro da ita ta adana gawarwaki tsawon kwanaki ko watanni ko ma shekaru na da illa kuma tana janyo wa ci yankinmu koma-baya, tabarbarewar tarbiyya da ma kowacce irin lalacewa,” inji sanarwar ta IPOB.