✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC Ta Kama Ma’aikata 23 Masu Yi Wa Mutane Rajistar Bogi

Za mu ci gaba da kare martaba da ingancin rajistar masu kada kuri’a.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce ta fara daukar mataki kan ma’aikatanta da ta samu da aikata laifuka a aikin rajistar masu zabe.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana hakan a taron da Hukumar ta gudanar a Abuja tare da jam’iyyun siyasa.

Yakubu ya ce INEC za ta dauki dubban ma’aikatan da za su ci gaba da aikin rajistar da a ka fara tun ranar 28 ga watan Yuni, a kammala ranar 31 ga watan Yuli.

“Abin takaici ne a ce wasu ba su gudanar da aikinsu yadda ya kamata ba, har ta kai su ga yin rajistar bogi.

“Abin da ba su sani ba shi ne kowacce na’urar rajistar na amfani da wasu lambobi da aka ba wa kowanne ma’aikaci.

“Don haka da lambar za a yi amfani a tantance jimillar adadin mutanen da kowane jami’in ya yi wa rajistar.

“Wasu kuma sau 40 ko fiye suka yi yunkurin yin rajistar bogi, don haka irinsu yanzu mun gano mutane 23 da suka aikata hakan., kuma mun fara daukar mataki a kansu.

“Za mu ci gaba da kare martaba da ingancin rajistar masu kada kuri’a domin yana da matukar muhimmanci ga gudanar da sahihin zabe.

Farfesan ya kuma gargadi jam’iyyun siyasa da ‘yan takara, hadi da magoya bayansu da su guji janyo duk wata fitina a lokacin yakin neman Zaben 2023.