✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

INEC ta ayyana Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Adamawa

Hakan ya biyo bayan kwanga-gaba-kwan-bayan da aka yi

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ayyana Ahmadu Umar Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Adamawa.

Ya sami nasarar ce da kuri’a 430,861, inda ya doke babbar abokiyar karawarsa, Sanata Aisha Dahiru Binani, wacce ta sami kuri’a 396,788.

A cewar jami’in INEC mai kula da bayyana sakamakon a Jihar, Farfesa Muhammed Mele, hakan ya biyo bayan kammala tattara sakamakon zaben da aka yi ne tun a ranar Asabar din da ta gabata.

A baya dai an gaza samun wanda ya lashe zaben a na farko da aka yi ranar 18 ga watan Maris, inda dole INEC ta ayyana shi a matsayin wanda bai kammala ba.

Daga bisani bayan karasa zaben ranar Asabar, Kwamishinan Zaben Jihar, Farfesa Hudu Yunusa Ari, ya yi azarbabin bayyana Binani a matsayin wacce ta lashe shi, duk da a lokacin ba a kammala tattara sakamakon ba.

Sai dai daga bisani hedkwatar hukumar da soke ayyanawar, inda ta dakatar da Kwamishinan sannan ta turo aka karasa tattara sakamakon.