✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ina kallo ’ya’yana 4 da mahaifiyata suka kone kurmus a harin ’yan bindiga’

Matar da ta tsallake rijiya da baya tana kallo ’ya’yan hudu da mahaifiya ta kawunta ’ya’yansa suka kone kurmus

Wata mata da ta tsallake rijiya da baya ta bayyana yadda aka yi wa ’ya’yanta hudu da mahaifiyarta kisan gilla a kan idonta a harin da ’yan bindigar da suka kona matafiya da dama a Jihar Sakkwato.

Aminiya ta kawo rahoton yadda ’yan bindiga suka tare wata motar haya da ke kan hanyarta ta zuwa Kaduna a tsakanin Isa da Sabon Birnin Jihar Sakkwato, suka yi wa matafiyan kisan gilla.

Matar da ta tsallake mai suna Shafa’atu ta ce, “’Ya’yana hudu na rasa a abin — ’yan mata uku da jariri mai wata 1o; Ina kallo ’ya’yan hudu tare da mahaifiya ta kawuna da ’ya’yan ’yan uwana suka kone kurmus, su kuma ’yan bindigar suna kallo suna jin dadi.”

Ta ce da ganin motar ’yan bindigar, “Harbi kawai suka rika yi har sai da motar ta yi adungure sau uku sannan ta kama da wuta. Ni da mutum daya ne kawai Allah Ya kubutar muka tsira a motar bas din, amma sauran fasinjojin sun rasu daga baya a sakamakon raunin harbi.”

Shafa’atu ta ce mutum 33 ne a cikin motar — manya da kananan yara — lokacin da ’yan bindigar da ake zargin yaran kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ne suka tare ta.

Matar mai shekara 30 ta bayyana wa Aminiya abin da ya faru ne kafin rasuwarta  a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodio (UDUTHI), inda ake jinyar ta saboda raunukan da ta samu a harin ’yan bindigar na ranar Litinin a yankin Sabon Birni.

Tuni dai aka yi jana’izar Shafa’atu kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar.