✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ihedioha ya janye daga neman takarar gwamnan Imo

Janyewar Ihedioha ba za ta rasa nasaba ba da maye gurbin shugaban jam’iyyar PDP na kasa Iyorchia Ayu.

Tsohon gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, ya janye daga neman takarar gwamna a jam’iyyar PDP da ta shirya gudanar da zaben fidda gwaninta a ranar 15 ga watan Afrilu.

Wakilinmu ya ruwaito cewa janyewar Ihedioha ba za ta rasa nasaba da tsige shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorchia Ayu, wanda aka maye gurbinsa da Iliya Damagum, mataimakin shugaban jam’iyyar ta Arewa.

Ihedioha ya yi aiki a matsayin mai magana da yawun Ayu lokacin yana Shugaban Majalisar Dattawa a 1992.

Bayanai sun ce akwai tsamin dangartaka tsakanin tsohon gwamnan da Sakataren jam’iyyar na kasa, Sanata Samuel Anyanwu, wanda aka sa ran rikici nasu zai yi tasiri yayin zaben fidda gwanin na ranar 15 ga Afrilu.

Sai dai tun kafin a kai ga nan, wakilinmu ya ruwaito cewa Ihedioha ya bayyana ficewar sa ne a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar na kasa.

Tsohon gwamnan ya ce ya janye daga takarar ne saboda muradin jam’iyyar.

Da aka tuntubi mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Chibuike Onyeukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin amma bai yi karin bayani ba.

Ana iya tuna cewa, Ihedioha ya lashe zaben gwamna na 2019 a karkashin PDP amma Kotun Koli ta tsige shi a ranar 14 ga Janairu, 2020, wacce ta ayyana Gwamna mai ci Hope Uzodimma wanda ya zo na hudu a zaben a matsayin wanda ya yi nasara.