✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan muka gyara harkokin sufurinmu rijiyoyin mai za su rage tasiri – Babban Sakataren NSC

Babban Sakataren Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta kasa (NSC), Barista Hassan Bello ya bukaci a zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da bangaren sufuri,…

Babban Sakataren Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ruwa ta kasa (NSC), Barista Hassan Bello ya bukaci a zamanantar da tashoshin jiragen ruwa da bangaren sufuri, inda ya ce Gwamnatin Tarayya za ta iya mayar da rijiyoyin man fetur din kasar nan marasa tasiri idan ta gyara bangaren sufuri yadda ya kamata, ya dace da dabarun tsara kasuwancin.

Bello ya ce shugabannin Hukumar NSC sun dukufa wajen yin gyare-gyare a bangaren sufuri don gyara kurakuran da ake yi a bangaren sufuri domin mayar da harkokin kasuwancin kasar nan da kasashen duniya zuwa tafarkin da ya dace. 

Ya ce Hukumar NSC ta kuduri aniyar amfani da fiton jiragen ruwa wajen farfado da tattalin arziki, musamman a yanzu da kasar nan take fuskantar wasu matsaloli da suke tilasta ta fadada harkokin tattalin arzikinta.

Ya ce “Ba za ka samu wurin da ya fi dacewa don fadada harkokin tattalin arziki irin sufuri ba. Wani ya sha fadin cewa idan muka inganta harkokin sufurinmu suka daidaita, za mu iya kusanto da rijiyoyin man fetur ga jama’a, saboda sufuri zai iya samar da kudin kasafin kasar nan.”

Ya kara da cewa: “Mun bayar da gagarumar gudunmawa ga tasoshin jiragen ruwa, inda muke da masu tsara tattalin arziki. Lokacin da na kama aiki shekara biyu da suka wuce, na ce muna yin abubuwa da yawa domin tsabtace abubuwan da suke faruwa a tashoshin. Mun fara daidaita hanyoyin gudanar da ayyuka, kuma ina farin cikin shaida muku cewa an yi haka ta yadda kusan kowace hukumar da ke tashoshin jiragen wura ta san abin da ya kamata ta yi kamar yadda ake yi a sauran kasashen duniya.”

Injiniya Bello ya ce, Hukumar NSC tana da tsare-tsaren karfafa tashshin ruwa, inda ake aike dukan korafe-korafi daga tashoshin ta hanyar Intanet.  Ya ce tsarin hukumar ce ita kadai ta samar da shi, kuma ya ce Hukumar Saukaka Harkokin Kasuwanci da ke ofishin Mataimakin Shugaban kasa ta rungume shi.

“Yanzu ta zama wani tsari na masana’antar kuma mutum na iya bibiyar korafe-korafe ko sharhi kana bin da ya shafu tsarin. Abin da muke kokarin yi, shi ne mu samar da ingancin aiki da tabbatar da gaskiya da rikon amana da haba-haba da abokan hulda da kuma gasa a tsakanin tashoshin jiragen ruwan Najeriya ta yadda Najeriya za ta zama uwa a Afirka ta Yamma da ta Tsakiya. Muna karbar karin manyan jiragen ruwan dakon kaya fiye da yadda sauran tashoshin ke yi. Muna gas ace da sauran tashoshin jiragen ruwa, musamman tashar Kwatano, kuma ba za mu bari su tsere mana ba.”

Game da karkatar da manyan jiragen ruwan dakon kaya zuwa wasu tashoshin jiragen ruwa na Afirka ta Yamma, Babban Sakataren ya ce, masu fiton jiragen suna da ’yancin daukar jiragen dakon kayansu zuwa kowce tashar jiragen ruwa, tun da lamarin ya shafi yanke shawara ce ta tattalin arziki.

“Ina farin cikin shaida muku, tunda Hukumar NSC ta fara wannan aiki na tsara ka’idoji da sanya ido, muke ta kawo manyan jiragen ruwan dakon kaya zuwa Najeriya. Hatta makwabtanmu kamar Nijar da Chadi yanzu suna kawo jiragen ruwan dakon kayansu zuwa tashoshin ruwan Najeriya. A baya suna kaiwa jiragen ruwa dakon ne zuwa Ghan da Kwaddibuwa da Togo. Bukatar yin gasa yana da matukar muhimmanci, don haka akwai bukatar mu inganta ayyukanmu. Abubuwa da dama za a inganta su kuma muna samun goyon bayan Ma’aikatar Sufuri ta Tarayya da Hukumar Kula da Tashoshin Ruwa ta Najeriya, tare da muhimman abokan hadin gwiwarmu kamar masu gudanar da tashoshin da kamfanonin fiton kaya ta ruwa da masu sauke kaya da masu dako daga tashoshin da sauran masu ruwa-da-tsaki a tashoshin za mu cimma nasara,” inji shi.

Bello ya nanata bukatar da ke akwai a kan Najeriya kan ta samar da ingantattun na’urorin da za a hada su da tsarin sufuri mai gaskiya, inda ya ce, babu bukatar sai ka je tashar jiragen ruwa kafin ka karbo kayanka inda hakan zai rage cakuduwar mutane.

Ya ce, “Za mu yi irin abin da ke faruwa a sauran kasashen duniya, inda za ka zauna a ofishinka ka biya duk abin da ake bukata ka karbi kayanka daga tashohin jiragen ruwa, kuma muna kan hanyar yin haka. Muna samu hadin kai daga Hukumar Kwastam ta Najeriya da kuma Rundunar ’Yan sandan Najeriya.”