✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Idan Buhari ya rattaba hannu a kan Kasafin Kudi na 2022…

Sauyin da sa-hannun Buhari a kan kasafin zai kawo a rayuwar talakan Najeriya

Juma’ar nan da hantsi ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai rattaba hannu a kan kudurin Kasafin Kudi na 2022.

Ana saura kusan mako guda shekarar 2021 ta kare ne dai Majalisar Dokoki ta Kasa ta aike da kudurin Kasafin zuwa Fadar Shugaban Kasa, bayan ta kara shi daga Naira tiriliyan 16.391 zuwa Naira tiriliyan 17.126.

Idan har Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan kudurin kamar yadda mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya ce zai yi, to za a samu ci gaba a tsarin aiwatar da kasafin kudi a Najeriya daga watan Janairu zuwa watan Disamba a duk shekara.

Sai dai kuma wani batu da mai yiwuwa zai fi damun talakan Najeriya shi ne: wanne alfanu zai samu daga kasafin don kawai shugaban kasa ya dora alklami a kan takarda ya yi watsattsake?

Alfanu ga talaka

Dokta Abdussalam Kani masanin tattalin arziki ne a Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimia da ke Kano; ya shaida wa Aminiya cewa daga ranar 1 ga watan Janairun sabuwar shekara, wato 2022, talaka zai iya samun sauyin rayuwa idan har aka yi amfani ko aka aiwatar da tsare-tsaren da Kasafin Kudin ya kunsa.

“Idan za mu iya tunawa a lokacin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yake gabatar da Kasafin Kudin a gaban Majalisa, ya bayyana wasu abubuwa da ya kira da manyan bukatu wadanda suka hada da rage talauci da inganta rayuwar al’umma da sauransu.

“Wadannan abubuwa ne da za su inganta rayuwar talakawa tare da kawo musu sauyi mai kyau”, inji shi.

Haka kuma Dokta Kani ya bayyana cewa Kasafin Kudin zai kawo alfanu sosai ga kasa ta hanyar ci gaba ko dorawa a kan ayyukan da aka faro da kuma gina tattalin arziki a kan wasu bangarorin da ba na man fetur ba.

Ana kukan targade…

Ganin cewa ana kukan targade, sai ga karaya ta samu – ma’ana, wasu na ganin kudin da aka yi hasashen kashewa a Kasafin sun yi yawa saboda karancin kudin shiga, sai ga Majalisa ta ma yi kari a kan abin da aka kasafta tun farko – ko me zai faru ke nan?

Wasu masana dai na ganin wasu daga cikin hanyoyin da aka bayyana za a samo kudin da aka yi hasashen kashewa sun cancanci yabo, amma sun yi kira da a kara kaimi wajen samar da karin hanyoyin samun kudi baya ga man fetur, wanda ke samar da kashi 80 cikin 100 na kudin shigar kasar.

A cewar Dokta Abdussalamm Kani ta hanyoyi biyu za a iya samun kudaden da ake hasashen kashewa wajen aiwatar da wannan Kasafin Kudin.

“Na farko, akwai bangaren man fetur wanda idan har za a rika hako gangar mai miliyan daya da dubu dari tare da sayar da shi a kasuwar duniya a kan Dala 65, to za a samu abin da ake bukata.

“Na biyu kuma shi ne ta hanyar harajin da ake tattarawa a cikin gida daga wasu kamfanoni da kuma abin da za a karba daga wasu hukumomin gwamnati masu ta’ammali da kudi kai-tsaye kamar su Hukumar Hana Fasa Kwauri da sauransu – hukumomin da yawansu ya kai 63.

“Haka kuma za a iya neman bashi daga gida zuwa na waje; wadannan su ne kadan daga hanyoyin da gwamnati take sa ran samun kudin da take hasashen kashewa a Kasafin Kudin.”

Da sauran rina a kaba

Har ila yau, Dokta Kani ya ce zai iya yiyuwa Shugaban Kasa ya yi kwarya-kwaryar Kasafin Kudi matukar bukatar hakan ta taso.

“Ya kamata jama’a su fahimci cewa shi yin kwarya-kwaryar kasafin kudi bayan Shugaban Kasa ya sanya hannu a kan kasafin kudin da ya fara kai wa Majalisa  abu ne da ke kan hanya domin dokar kasa ta ba shi damar yin hakan.

“Idan har ya zamana Shugaban Kasa yana son canza ko matsar da wasu kudi zuwa wasu wuraren ko kuma idan wasu kudi suka shigo wa gwamnati wadanda ba a sanya su a Kasafin Kudin ba to dole sai ya nemi sahalewar Majalisa kafin ya yi wani abu a kai.

“Don haka idan har bukatar hakan ta taso wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari to zai iya sake mika wa Makalisar kwarya-kwaryar kasafin kudi”.

A baya dai Shugaba Buhari ya rattaba hannu a kan Kasafin duk da korafin da ya yi a kan karin da Majalisar Dokoki ta yi a kan abin da ya gabatar, yana mai cewa zai tura kwarya-kwaryar kasafi don daidaita lissafi.

Galibin kudin da aka kasafta kashewa za su tafi ne wajen biyan albashi da sauran bukatun ma’aikata.

Ranar Larabar makon jiya ne dai Majalisar Dattawa ta amince da Kasafin Kudin na 2022, yayin da Majalisar Wakilai ta amince da shi kwana guda kafin nan.

Wata takarda da Akawun Majalisar Dokokin, Mista Amos Ojo, ya sanya wa hannu ta nuna cewa tun ranar Juma’ar makon jiya aka aike da Kudurin Kasafin ga Shugaba Buhari.