Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ta gurfanar da wasu ma’aikatan gwamnati biyu, kan karkatar da Kuɗaɗen da Bankin Duniya ta bayar na gyaran makarantu.
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta (ICPC) ta gurfanar da wasu ma’aikatan gwamnati biyu, Popoona Samuel da Arama Davies Gyandi, a Babbar Kotun Tarayya dake Yola.
Suna fuskantar tuhume-tuhume guda hudu na halasta kudin haram da kuma rike kudaden da aka samu ta hanyar aikata laifuka.
Waɗannan kudade, da suka kai Naira miliyan 4.9, ana zargin an karkatar da su ne daga kudaden da Bankin Duniya ya ware don gyaran makarantun da rikicin ’yan tada kayar baya ya shafa a Jihar Adamawa.
Samuel da Gyandi, waɗanda suka yi aiki a karkashin Aikin Zuba Jari na Ilimi na Jiha a Ofishin Akanta-Janar na Jihar Adamawa har zuwa shekarar 2020.
Ana zargin su da haɗa baki wajen halasta kuɗaɗen da suka mallaka daga kwamitocin gudanarwa na makarantun firamare.
Musamman, an zargi Samuel da karɓar Naira miliyan 2.4 daga Makaranta Firamare ta Kwaja da kuma Naira miliyan 2.5 daga Makarantaar Firamare ta Mutuku, inda ya tura Naira miliyan ɗaya na kudin Kwaja ga Gyandi.
Duk waɗannan kuɗaɗen wani bangare ne na aikin gyaran makarantu na Bankin Duniya.
Waɗanda ake tuhumar sun musanta dukkan zargin.
Lauyan ICPC ya nemi kotu ta sanya ranar shari’a, yayin da lauyan masu kare su ya nemi beli.
Kotu ta bayar da belin su a kan Naira miliyan 5 tare da mai tsaya masa guda ɗaya, wanda dole ne ya zama ma’aikacin Gwamnatin Tarayya ko Jihar Adamawa (mataki na 14 zuwa sama), ko sarkin gargajiya (Hakimi ko sama da haka), ko kuma daraktan kamfani mai jari akalla Naira miliyan 10.
Sauran sharuɗan sun haɗa da hotunan fasfo na kwanan nan, da sauran takardu da kuma tabbatar da adireshin mazaunin mai tsayawar.
An dage shari’ar zuwa 22 ga Oktoba, 2025, don fara sauraron karar.