✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ibrahim Abdulaziz na Muryar Amurka ya rasu

Allah Ya yi wa tsohon dan jaridar Dailytrust, Ibrahim Abdulazeez rasuwa. Ibrahim Abdulaziz kafin rasuwarsa wakilin gidan Radiyon Muryar Amurka (VOA) ne  a Yola, Jihar…

Allah Ya yi wa tsohon dan jaridar Dailytrust, Ibrahim Abdulazeez rasuwa.

Ibrahim Abdulaziz kafin rasuwarsa wakilin gidan Radiyon Muryar Amurka (VOA) ne  a Yola, Jihar Adamwa.

Ya rasu ne sakamakon hataarin mota tsakanin Alkaleri da Bauchi, ya rasu ya bar mata da yara.

A lokacin rayuwarsa, Ibrahim Abdulazeez, ya yi aiki da gidan Rediyon Liberty, a matsayin babban wakilinta a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ya kuma yi aiki da gidajen rediyon Gotel da Fombina FM Yola, mallakin Gwamnatin Tarayya, kuma shi ne kuma mawallafin jaridar Adamawa Times.

Kafin nan, ya kuma yi aiki da gidan rediyon Nagarta da ke Kaduna.