✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar yaki da cin hanci ta gayyaci Sarki Sunusi

Hukumar kula da korafe-korafen jama’a da kuma yaki da cin hanci ta jihar Kano ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, domin amsa zargin sama…

Hukumar kula da korafe-korafen jama’a da kuma yaki da cin hanci ta jihar Kano ta gayyaci Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, domin amsa zargin sama da fadi da Naira biliyan 2.2.

Rohotanni sun bayyana cewa, Sarkin yana fuskantar sabbin bincike daga hukumar bisa zargin sayar da filayen masarautar ba bisa ka’ida ba.

Ana sa ran Sarkin mai daraja ta daya zai bayyana a gaban hukumar a ranar Alhamis, domin amsa tambayoyi akan zarge-zargen wadanda suka ci karo da sashe na 22, 23 da kuma 26 na dokokin hukumar.

An bayyana hakan ne a wata wasikar gayyata wacce ke dauke da sa hannun shugaban hukumar, Mista Muhuyi Magaji Rimingado, wanda aka rabawa manema labarai a Kano ranar Laraba.

Wasikar gayyatar ta ce, “Hukumar tana binciken zargin karan tsaye ga sashe na 22, 23 da 26 na kundin dokar hukumar kula da korafe-korafe da yaki da cin hanci ta shekarar 2008, a kula da filaye da aka killace a matsayin “Gandun Sarki” a fadin jihar.”

Tuni dai wasikar ta isa masarautar inda Daraktan Sashen aiyuka na musamman da sadarwa na hukumar, Usman Bello ya bayyana wa ‘yan jaridu hakan a ranar Laraba.

Bello ya kuma bayyana cewa an faro binciken ne bayan wasu sun kwarmatawa hukumar abinda ke faruwa. Ya ce, sashe na 31 na dokar da ta kafa hukumar ta bata ikon gayyata da kuma binciken sarkin aka zargin da ake masa.

Bello ya kara da cewa, bincikensu ya gano cewa wani kamfani mai suna Country Wide House Ltd ta taimaka wajen karkata kudade da suka kai Naira miliyan 520 na wani fili mai fadin hekta 20 a Darmanawa II.

A bayaninsa an siyar da filin ne ba bisa ka’ida ba, ga wani kamfani mai suna ‘Messrs Family Home Fund Limited’ inda ake zargin Sarkin yana da masaniya.

Ya ce, zargin kulla cinikin saida filayen masarautar a Darmanawa, Hotoro da Bubbugaje an yi shi ne da sa hannun wasu mutane uku da suka hada da: Shehu Muhammad Dankadai (Sarkin Shanu), Sarki Abdullahi Ibrahim (Makaman Kano) da Mustapha Kawu Yahaya (Dan Isan Lapai) bisa umarnin masarautar.

An dai gayyaci mutanen uku kuma suka bayyana a gaban hukumar a lokuta daban-daban kuma sun bada muhimman bayanai.

Mai Magana da yawun hukumar, Bello Usman ya kuma bayyana cewa Sarkin ya bada umarnin a biya Naira miliyan 175 ga kamfanin ‘Messrs Apple Integrated Resources’, inda ya kaucewa matakin da aka yanke a taron hukumomin masautar da aka yi a shekara ta 2016.

Ya kara da cewa, wasu manyan Kansilolin masarautar sun bada hadin kai saboda gabatar da binciken. A saboda haka ne hukumar ta gayyaci Sarkin da ya bayyana a gabanta saboda ya bada karin bayani a ranar 5 ga watan Maris na shekara ta 2020.

Idan dai za’ayi iya tunawa, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano tayi watsi da rahoton hukumar da ya nuna cewa Sarkin ya yi sama da fadi da kudi Naira biliyan 3.4 na masarautar.

Kotun dai ta bayyana cewa ba’a bai wa Sarkin daman kare kansa ba. A halin yanzu dai akwai kararraki biyu a gaban kotun game da zargin sama da fadi da Naira biliyan 3.4 da hukumar take zargin Sarkin ya yi.

Majalisar Kano ta kafa kwamitin binciken Sarkin Kano

Ganduje ya bude wani sabon bincike kan Sarkin Kano

Ganduje ya gindaya sharudda akan sulhunsu da Sarkin Kano