Hukumar Bunkasa kasashe ta Majalisar dinkin Duniya (UNDP) ta kai daukin ayyukan daban-daban ga fiye da al’ummu dubu 50 a yankin Arewa maso Gabas. Babban jami’in hukumar a Najeriya, Mista Yoshi Nugochi ne ya bayyana haka a Gombi da ke Jihar Adamawa a ranar Juma’ar da ta gabata, lokacin da ayarin Gwamnatin Tarayya ta ziyarci inda ake ayyukan jinkai da Hukumar UNDP ta gudanar a jihar.
Ayarin yana karkashin jagorancin Babbar Mataimakiyar Jami’in Tsare-Tsare na Ma’aikatar Kasafi da Tsare-Tsare, Madam Margaret Dibigbo. Nugochi ya ce akalla al’ummu dubu goma da yakin Boko Haram ya shafa ne suka samu ayyukan tallafin jinkai daban-daban a Adamawa.
Ya lissafo wasu daga cikin ayyukan jinkan da aka gudanar da suka hada da tallafin kayayyakin noma da na koyar da sana’o’i da gyara asibitoci da dakunan shan magani da sauransu.
A yayin da take maida jawabi, Madam Dibigbo ta yaba wa Hukumar UNDP kan rawar gani da ta taka wajen inganta rayuwar al’umma a Adamawa. Sannan ta nuna gamsuwa kan ayyukan jinkan, inda ta ce ayyukan tallafin jin kan za su canza rayuwar al’ummomin da ke kauyukan matuka. Sannan sai ta yi kira ga Gwamnatin Japan ta samar da karin kudi ga shirin ta yadda zai isa ga karin jama’a a sassan jihar. Haka kuma ayarin ya kai ziyara ga Asibitin Guyuk da wuraren gudanar da kananan sana’o’i da manoman shinkafa da kungiyoyin gama-kai na mata a kananan hukumomin Gombi da Hong da Girei da Michika da Madagali.