A kokarinta na inganta tsarin sufuri a tashoshin jiragen ruwa, Hukumar Sufurin Jiragen Ruwa ta Najeriya (Nigerian Shippers’ Council) ta bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da an daukaka harkar sufurin ruwa zuwa na zamani.
Babban Sakataren Hukumar, Barista Hassan Bello ya yi kiran lokacin da hukumar ta kai ziyarar musamman ga kungiyar ’Ya Kasuwa da Masu Masana’antu ta Legas (LCCI), a ranar Talatar makon jiya.
Barista Bello ya ce zamanantarwar za ta kawo karin kudin shiga ga Gwamnatin Tarayya tare da rage gwamutsuwar mutane da kuma magance wasu abubuwa da ba su dace ba da ake gudanarwa a tashoshin jiragen ruwan kasar nan.
Ya bayyana tashoshin jiragen ruwan Najeriya da wadanda suke gogayya da sauran na duniya, inda ya ce kalubalen da ake fuskanta ne ya jawo bukatar zamanantarwar da za ta yi amfani, yana mai cewa masu zuba jari za su so su rika huldar kasuwancinsu a tashoshin jiragen ruwa masu dadin harka.
Babban Sakataren ya ce Gwamnatin Tarayya ta dora wa hukumar nauyin tsara harkokin tattalin arzikin tashoshin jiragen ruwan tare da daidaita ayyukan tashoshin da kuma tsara yadda za a inganta tafiyar da tashoshin jiragen ruwan Najeriya.
Tun farko Shugaban kungiyar ’Yan Kasuwa da Masu Masana’antu ta Legas, Dokta (Misis) Nike Akande ta bayyana farin ciki kan ziyarar da Bello da jami’ansa suka kai ziyara ga LCCI din.
A cewar Misis Akande kungiyar ta ji dadi lokacin da jami’anta suka samu labarin shirin sake fasalin harkokin tattalin arzikin tashoshin jiragen ruwa da Hukumar NSC ke gudanarwa. “Ina taya ku murna kan daukaka matsayinku zuwa ta wata hukumar mai tsara harkoki a fannin sufurin jiragen ruwa. Wannan babban sauki ne ga mambobinmu. ’Yan kasuwa suna bukatar a rika ba su kariya daga masu gudanar da harkoki daban-daban, musamman abin da ya shafi karbar haramtattun haraji,” inji ta.
Ta bayyana himmar kungiyar LCCI ta bayar da goyon baya ga yunkurin Hukumar NSC na mayar da Najeriya wata cibiyar harkokin sufurin jiragen ruwa da ke haba-haba da masu zuwa jari.