Mahukunta Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NSC), ta bukaci hadin kan Rundunar ’Yan sandan Najeriya domin ta samu damar gudanar da ayyukanta yadda ya kamata.
Babban Sakataren Hukumar NSC, Barista Hassan Bello ne ya yi kiran lokacin da ya karbi bakuncin Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya mai kula da ’Yan sandan Tashoshin Ruwa, Felid Ogundeji a hedkwatar hukumar da ke Apapa, Legas.
Barista Bello ya ce, “Muna bukatar karin jami’an tsaro. Kuma ina jin zai yi kyau idan muka yi haka kamar yadda doka ta tanada,” a matsayin wani rigakafin duk wata tawaye wajen gudanar da ayyukanta na tabbatar da ana bin dokoki a tashoshin jiragen ruwan.
Ya ce a wasu lokuta ma’aikatan hukumar za su bukaci taimakon ’yan sanda yayin da suke gudanar da aikinsu na lura da tashoshin yadda ya kamata.
“Akwai bukatar mu tattauna a kan taimakon da za ku iya ba mu. Mun samu hadin kan masu kula da wuraren sauke kaya da kamfanonin jiragen ruwa da dillalan fiton kaya da sauran hukumomin gwamnati. Kuma mun tattauna da damansu wasu saboda muna da akidar jin ta bakin masu ruwa-da-tsaki. Dole za a rika samun masu karya dokoki da za su hana mu gudanar da aikinmu, duk da cewa sun san doka ce ta dora mana wannan nauyi,” inji Bello.
Ya kara da cewa, duk da cewa ’yan sandan tashohin jiragen ruwa su ma masu ruwa-da-tsaki a masana’antar, “Har yanzu muna samun korafe-korafe a kan ’yan sandan game da binciken jiragen da aka wanke su daga tashohin ruwa.”
Babban Sakataren ya ce hukumar za ta so ’yan sandan tashoshin ruwa su rika gudanar da irin ayyukan da suke yi a Tashoshin Tudu (IDCs) da zarar sun fara aiki.
Bello ya ce hukumar ta tattauna da bangarori da dama na ’yan sandan, kuma an magance irin wadannan matsaloli.
“A wajen ayyukanku na yau da kullum, idan aka samu zargi mai karfi, ’yan sanda za su iya gudanar da bincike idan suka yi tunanin ana kokarin aikata barna ko an aikata,” inji shi.
Barista Bello ya yaba wa Gwamnatin Tarayya kan yadda ta fadada harkokin tattalin arziki maimakon dogaro da mai.
“Muna duba yanayin ayyukan raya kasa da kirkiro ayyukan samun kudi da bunkasa tattalin arziki da samar da ayyukan yi da kuma samar da ingantattun harkokin kasuwanci irin na duniya. Aikin Hukumar NSC shi ne samar da daidaito ta yadda ’yan Najeriya za su ci moriyar albarkatun sufurin jiragen ruwa,” inji shi.
Da yake mayar da jawabi, Mista Ogundeji ya bayyana hukumar da rundunar ’yan sandan tashohin jiragen ruwa da abokan aiki a harkokin kula da tsaron ruwan Najeriya, inda ya ce idan aka yi aiki tare, za a samu nasarar abin da kasar take bukata tsaron ruwan Najeriya tare da bayar da gudunamawa wajen sauke nauyin da aka dora wa hukumar.
Mataimakin Sufeto Janar ya ce, “Rigakafin miyagun ayyuka da kare ruwan Najeriya babban aiki ne. kalubalen da ke cikin kula da teku mai girma da yawa ne. Kuma gwamnatin ba ta mayar da hankali a ka haka yadda ya kamata.”
“Kuma mun gano cewa aikin da ke kanmu na tsaron ruwan Najeriya ba zai gudana ba ba tare da neman hadin kan masu ruwa-da-tsaki ba,’ inji shi.
Ya nuna cewa akwai bukatar a samar da kyakkyawan yanayi ga masu niyyar amfani da ruwan Najeriya.