Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) tare da hakin gwiwar Hukumar Bayar Da Tsaro Ta Farin Kaya (NSCDC) sun kulla wata yarjejeniya na ganin sun dakile batagari daga barnata kayayyakin gwamnati da na kamfanonin sadarwa a fadin kasar nan.
Hukumomin biyu sun kulla wannan yarjejeniyar ce a Hedkwatar Hukumar NCC da ke Abuja, inda Shugaban Hukumar NCC Farfesa Umaru dambatta ya sanya hannu a madadin hukumarsa yayin da Shugaban Hukumar Bayar Da Tsaro Ta Farin Kaya (NSCDC) Abdullahi Muhammadu ya sanya hannu a madadin hukumarsa.
A kwanakin baya ne Gamayyar kungiyoyin Kamfanin Sadarwa ta Najeriya (Association of Telecomunnication Operators of Nigeria (ALTON) ta kai wa Hukumar NCC ziyara a ofishinta da ke Abuja inda suka koka a game da yadda bata-gari ke yawan lalata musu kayayyakin sadarwa da hakan yake shafar igancin sadarwa a Najeriya.
A lokacin da yake jawabi, jim kadan bayan sun kulla yarjejeniyar, Farfesa Umaru dambatta ya ce akwai bukatar su hada kai da jami’an tsaro wajen ganin sun kare kayayyakin kamfanonin sadarwa da ke fadin kasar nan don a ba su damar gudanar da aikinsu cikin natsuwa da kuma kwanciyar hankali.
“Idan idan muka samu nasarar yin haka, to wata hanya ce da za mu taimaka wa gwamnati a kokarinta na bunkasa tattalin arzikin kasa”, inji shi.
Ya ce idan aka samar da tsaro a bangaren harkar sadarwa, ko shakka babu za a samu masu rububi wajen zuba jari a bangaren sadarwa. A kan haka ya ce za a bude Hukumar NCC ta kuduri aniyar bude ofisoshin da za su rika kula da na’urorin kamfanonin sadarwar a kowane lungu da sako na kasar nan, da hakan zai bayar da kariya ga lafiyar al’umma da kuma ta na’urorin a kowane lungu da kuma sako na kasar nan.
“Mun sha nanata wa ’yan Najeriya cewa muna da kudurori 8 da muke da muke yunkirin aiwatar da su a bangaren sadarwa daya daga ciki shi ne hada kai da wasu daga cikin hukumomin gwamnati wajen samar da tsaro a bangaren sadarwa”.
“Don haka saboda muhimmancin da harkar sadarwa ke da shi a Najeriya ne ya sanya muka kulla yarjejeniya da Hukumar Samar da Tsaro Ta Farin Kaya Ta Najeriya (NSCDC) inda za mu ci gaba da sanya ido wajen ganin batagari ba su samu damar lalata wa kamfanin sadarwar kayayyakinsu ba da kuma na ofisoshin sauraron koken jama’a da hukumar NCC za ta samar a kowane bangare a kasar nan.
dambatta ya ce tuni suka kammala shirye-shiryen samar da irin wadannan ofisoshin da za su rika sanya ido wajen kare kayayyakin don haka za a iya tuntubarsu da zarar wani bala’i ya auku, don haka ofis ne da zai rika hulda da jama’a da kuma na kamfanonin sadarwar.
“Wannan yarjejeniyar da muka kulla ta nuna kudurin da muke da shi na samar da ingantaccen tsaro ga ’yan Najeriya kamar yadda za mu kare kayayyakin kamfanonin sadarwa a dukkan fadin kasar nan”.
“Tuni shugaban Hukumar NSCDC ya ba jami’ansa umarni su fara gudanar da aiki na bayar da kariya ga kayayyakin sadarwar a fadin kasar nan, kuma wannan abin a yaba ne”.
“Dalilin da ya sa Hukumar NCC ta gayyato Hukumar NSCDC wajen bayar da kariya ga kayayyakin kamfanonin sadarwa a kasar nan shi ne, bangaren sadarwa ne yake samar da kashi 8 zuwa 10 na kudin shigar Najeriya da hakan ke nuna yana samar da akalla Naira Tiriliya 1 da Miliyan 600 a kowane watanni uku. Sannan bangaren sadarwa ne ya fi shafar kowane bangare na tattalin arziki, don idan babu sadarwa, to harkoki za su tsaya cik.
Mutane da dama sun zuba jari a harkar sadarwa, wasu ma suna da niyyar zuba jari amma matsalar da muke fuskanta a yanzu ita ce na yadda batagari suke bata wa kamfanonin sadarwa na’urorinsu da hakan yake kawo nakasu da kuma jefa tsoro a zukatan masu son zuba jarin, da ma wadanda suka riga suka zuba jarin”.
A nasa jawabin, Shugaban Hukumar NSCDC Abdullahi Gana Muhammadu ya yaba da tayin da Hukumar NCC ta yi musu na su hada kai wajen yaki da batagarin da ke lalata kayayyakin sadarwa a fadin kasar nan. Shugaban ya kara da cewa an kirkiro da Hukumar NSCDC ce don bayar da kariya ga kayayyakin gwamnati da na kamfanoni masu zaman kansu. Ya ce hasalima an kafa hukumarsu ce don su rika tallafawa hukumomin tsaro na ’yan sanda da kuma na soji da ke fadin kasar nan.
Daga nan ya ba Shugaban Hukumar NCC tabbacin NSCDC za ta yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta bayar da kariya ga kayayyakin kamfanonin sadarwa da ma samar da tsaro ga dukkan bangarorin da ke fadin kasar nan ba tare da gajiyawa ba.
“Ina mai tabbatar maka zan yi amfani da jami’ai na ta hanyar ba su bindigogi da alburusai don su bayar da kariya ga kayayyakin kamfanonin sadarwa a fadin kasar nan”.
“Kodayake muna fama da karancin bindigogi da alburusai da kuma na ma’aikata, amma duk da haka ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen samar da tsaro a kasar nan”.
“Yanzu haka akwai batagarin da muka kama wadanda ke fuskantar shari’a a kotu, amma ba zan bayyana sunanyensu ko wurin da suke fuskantar shari’ar ba saboda dalilin tsaro”.
Ya juya jiya akwai wasu batagari biyar da suka gurfana a gaban wata kotu da ake zarginsu da fasa bututun mai a yankin Kudu maso Gabas”.
A wani labara makamancin wannan, shugaban Hukumar NCC ya nuna damuwarsu a kan yadda wasu ke amfani da layukan waya da ba a yi musu rajista ba, inda ya ce wannan lamarin zai iya janyo matsala ga harkar tsaron kasar ba ma hukumar kadai ba.
Ya yi gargadin cewa ko dai a daina, ko kuma a fuskanci fushin hukuma, inda ya ce hukumar ba za ta zura ido tana kallon yadda wasu kalilan mutane suna wargi da harkar tsaron kasar nan ba.
“Ba za mu zuba ido muna kallon wasu kalilan a cikinmu suna amfani da layukan waya da ba su da rajista ba, domin yana janyo tarnaki ga harkar tsaron kasar. Dole mu yi duk abin da za mu iya yi domin dakatar da amfani da layukan da ba a musu rajista ba. Ina gargadin wadanda suke amfani da irin wannan layukan wayar da su bari ko kuma su fuskanci fushin hukuma.
“Za mu yi duk mai yiwuwa wajen hana kasuwancin irin wannan layukan. Mun fara aiki a kan hakan, baya ga amfani da fasahar zamani wanda zai taimaka wajen nuna misali ga wadanda suke amfani da layukan cewa suna zamba cikin aminci,” inji shi.