✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Kwastam ta nada sabon Kakaki

Yana da digiri na uku a harkar jarida.

Hukumar Hana Fasa Kwauri wato Kwastam ta nada Abdullahi Aliyu Maiwada a matsayin sabon mai magana da yawun hukumar.

Shugaban Hukumar Kwastam na Kasa, Kanal Hameed Ibrahim Ali mai ritaya ne ya ba da umarnin nada CSC Maiwada bayan duba nagarta da kuma iya aikinsa shekara da shekaru a hukumar.

Maiwada dai ya taba zama kakakin hukumar na Shiyya ta biyu ta Hukumar Kwastam da ke Kaduna ya kuma rike wannan mukami a Jihar Ogun da ke Arewa maso Yamma na tsawon shekaru.

Ya dawo shalkwatar hukumar a shekarar 2020 inda ya zama jami’in hulda da ke tsakanin gidan jarida na Kwastam da jami’an kwastam a bangarorin Najeriya.

Maiwada ya yi digirinsa na farko a Jami’ar Bayero a yanzu yana da digiri na biyu guda biyu kuma yana digiri na uku a harkar jarida.