✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar FAO ta fara ba da tallafin gaggawa kan noman rani a Arewa maso Gabas

Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar dinkin Duniya (FAO) ta kaddamar da shirinta na tallafin gaggawa kan noman rani don inganta rayuwar jama’a a jihohi…

Hukumar Abinci da Noma ta Majalisar dinkin Duniya (FAO) ta kaddamar da shirinta na tallafin gaggawa kan noman rani don inganta rayuwar jama’a a jihohi uku da suka fi haduwa da bala’in yaki da Boko Haram a Arewa maso Gabas na Najeriya. Manufar shirin a fadada da inganta samar da abinci tare da karfafa jajircewar mutane a lokacin da suke fuskantar rikici. Kimanin iyalan manoma dubu 117 (da suke wakiltar mutum dubu 760) ne ake sa ran su ci gajiyar wannan tallafi.

Manoman sun karbi irin shuka da shinkafa da takin zamani tare da injunan ban ruwa, kuma sun samu horo tare da tallafin gudanar da kananan lambuna don kara yin noma da rage illar karancin abinci tare da inganta samar da abinci mai gina jiki ga iyalan da suke fuskantar yunwa.

Kamfe di nana aiwatar da shi ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi kuma an kaddamar da shi ne a wani biki da aka gudanar a Maidguri, Jihar Borno a karkashin jagorancin Gwamna Kashim Shettima. A Yola, Jihar Adamawa, Gwamna Muhammadn Umaru Jibrilla Bindow ne ya kaddamar da shirin. Sai kuma Jihar Yobe inda Kwamishinan Aikin Gona, Mustapha Gajerima ya wakilci Gwamna Ibrahim Gaidam wajen kaddamar da shirin.

Wakilin Hukumar FAO a Najeriya, Mista Suffyan Koroma, ya halarci kaddamar da shirin a dukan jihohin inda ya nanata cewa, “Tallafin Hukumar FAO ga samar da abinci ga mazauna Arewa maso Gabashin Najeriya yana mayar da hankali ne wajen taimaka wa al’ummun da rikicin Boko Haram ya shafa ta yadda za su farfado cikin gaggawa su cimma bukatunsu na abinci ta hanyar yin noma da kansu tare kuma da bayar da gudunmawa wajen karfafa jajircewarsu ga rikicin da ka iya tasowa.”

A bana Hukumar FAO ta taimaka wa mutane sama da miliyan daya da rabi, inda ta mayar da hankali kan mutanen da suke gudun hijira da wadanda suke komawa garuruwansu da masu masaukin ’yan gudun hijirar da suke jihohin Adamawa da Borno da Yobe a karkashin tallafin gaggawa. Tallafin Hukumar FAO wani yunkuri ne na tallafa wa kokarin gwamnatin na dawo da harkokin rayuwa da magance muhimman matsalolin da suka shafi karancin abinci da rashin abinci mai gina jiki a yankunan da ayyukan ta’addanci na Bokom Haram suka shafa. Yunkurin Hukumar FAO na karfafa jajircewar jama’a da gina duniyar da ta kubuta daga yunwa ya sanya ta samu nasara ce tare da tallafin kudi daga masu bayar da tallafi. Kudaden suna fitowa ne daga gwamnatocin kasashen Beljiyum da Cibiyar bayar da tallafin gaggawa ta Majalisar dinkin Duniya (CERF) da Hukumar ECHO da kasashen Faransa da Jamus da Ireland da Norway da hukumomin OFDA da SIDA da kuma kasar Switzerland.