✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar DSS ta musanta kama shugaban EFCC

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a najeriya, DSS, ta musanta cewa ta kama mukaddashin shugaban Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ta’annati, EFCC.…

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a najeriya, DSS, ta musanta cewa ta kama mukaddashin shugaban Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arzikin Ta’annati, EFCC.

Kafofin yada labarai a Najeriya dai sun ba da labarin cewa hukumar ta DSS ta kama Ibrahim Magu ranar Litinin.

Wata sanarwa mai dauke da sa-hannun Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Peter Afunanya,  ta ce babu kamshin gaskiya a labarin.

“Hukumar DSS na sanar da jama’a cewa ba ta kama Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar EFCC, ba kamar yadda wasu kafofin yada labarai ke yayatawa”, inji sanarwar.

Tun da farko wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa jami’an DSS din sun dirar wa hedkwatar hukumar ta EFCC da ke unguwar Jabi a Abuja ne da hantsi, inda suka yi awon gaba da Magu, bayan da a makonnin baya kokarin su na kama shi ya ci tura.

Zargin almundahana

Rahotannin kamun nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da Antoni Janar kuma Ministan Shari’a na Najeriya, Abubakar Malami, ya zargi Magu da hannu a wata badakalar kudade, ciki har da sauya akalar wasu kudaden da aka kwato.

Sai dai zuwa yanzu daga shugaban na EFCC har kakakin hukumar babu wanda ya ce uffan game da batun kamen nasa.

A baya dai Magun ya musanta aikata ba daidai ba, inda ya kwatanta zarge-zargen a zaman bi-ta-da-kullin siyasa.