✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotunan matsahin hafsan sojin da ya rasu a hatsarin jirgin Kaduna

Tuni aka yi jana'izarsa bisa tsarin addinin Musulunci.

An gano daya daga cikin hafsoshin Sojin Saman Najeriya da suka rasu bayan jirginsu ya yi hatsari a ranar Talata.

Daya daga cikinsu shi ne Abubakar Alkali, dan asalin Jihar Yobe ne, kuma ya kwanta dama ne bayan jirgin da shi da abokin aikinsa suke tukawa ya fadi a Sansanin Sojin Sama da ke Kaduna.

Ga wasu daga cikin hotunan Abubakar wanda tuni aka yi jana’izarsa bisa tsarin Musulunci:

Abubakar Alkali yana daukar kansa hoto a gaban wani jirgin soji.
Alkali a lokacin da yake karbar wata kyauta da ya samu saboda jajircewarsa.
Marigayi Abubakar Alkali a lokacin wani taro, rike da wata kyauta da ya samu.
Abubakar Alkali a kusa da jirgin yaki a wani sansanin soji, a lokacin rayuwarsa.
Shi ne a nan a lokacin wani faretin daurin auren wani abokin aikinsu.
Abubakar a cikin fararen kaya a wani filin jirgin sama a lokacin rayuwarsa.