✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta cafke matasa 19 kan kokarin shirya auren jinsi daya a Kano

Hisbah ta yi wa wajen dirar mikiya tun kafin daura auren Abba da Mujahid.

Wasu matasa 19 sun shiga hannun Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, kan kokarin hada auren jinsi daya a jihar.

Wadanda suka shiga hannun, da yawansu matasa ne sun yi kokarin daura wa wasu maza biyu masu suna Abba da Mujahid aure a matsayin miji da mata.

Jami’an hukumar sun yi wa wajen da za a daura auren dirar mikiya, inda suka damke mata 15 da kuma maza hudu.

Da yake tabbatar da kamen matasan, Babban Kwamandan hukumar, Sheikh Haruna Ibn Sina, ya ce amarya da angon (Abba da Mujahid) sun tsere bayan da jami’an Hisbah suka dira wajen.

Sai dai Ibn Sina ya ce wadda ta shirya bikin, Salma mai shekara 21 na hannun hukumar.

Amma ya ce hukumar na ci gaba da samamen wadanda suka tsere din don ta kama su.

Kwamandan ya ce tuni hukumar ta nutsa da bincike don gurfanar da wadanda suka shiga hannunta, wanda a cewar wasu daga cikinsu gayyatarsu aka yi zuwa wajen daurin auren.

Amma ya ce wasu daga cikin wadanda aka kama din sun roki da a yi musu sassauci bisa sharadin ba za su sake aikata laifin ba.