✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hauhawar farashin kaya na jawo mana asara —’Yan kasuwa

’Yan kasuwa sun ce yawancinsu jarinsu ya karye saboda hauhawar farashin.

Hauhawar farashin kayan masarufi da aka bayyana a matsayin mafi muni a tarihin kasar nan, na ci gaba da damun ’yan kasuwa da masu sayen kayan.

Wadansu ’yan kasuwa da Aminiya ta zanta da su da suka hada da wani jagora a katafaren kantin nan na Sahad mai rassa da dama a kasar nan, sun ce lamarin ba zai rasa nasaba da tashin farashin Dala da faduwar darajar Naira ba, kuma hakan ya yi sanadin karyewar takwarorinsu da dama.

Alhaji Shehu Lawan wani mai shagon sayar da fulawa da sukari da shinkafa a garin Kubwa, Abuja, ya ce ya sha yin cikon kudi, ciki har da ribar da yake jin ya samu, don ya sayo nau’in kaya da ya sayar kasa da mako guda daga kamfani ko kasuwanni.

Ya ce, “Na sayar da kananan buhunan garin samobita a kan Naira dubu biyar-biyar, bayan na sayo kowane daya a kan Naira dubu hudu da 900. Ina ganin na samu ribar Naira 90 a kan kowane buhu bayan na cire masa kudin mota Naira 10.

“Amma kasa da mako daya da na koma kasuwa, sai a ka ce mini farashin kowane buhu ya koma Naira dubu biyar da da 200. Haka na hakura da sayen wannan kaya a ranar saboda idan zan sake sari sai dai in sayi guda tara maimakon 10.”

Dan kasuwar ya ce munin matsalar ta fi kamari a bangaren garin fulawa.

Ya ce maigidansu da yake Kano ya biya kudin kaya sama da wata guda ga wani kamafani, amma ba tare da an aika masa da kayan ba.

“Da suka tashi ba da kayan sai suka ce sai ya yi karin Naira miliyan bakwai da wani abu, kuma dole sai da ya yi hakan saboda ba ya da zabi,” inji shi.

‘Ministar Kudi ta gaza’

Ya ce dole ne Ministar Kudi ta binciki matsalar hauhawar farashin idan kuma ba za ta iya magance matsalar ba, a sallame ta tare da nada wanda zai iya sa-ido a kan matsalar.

“Hujjar da kamfanoni suke ba mu a kullum ita ce tashin Dala, sun ce a baya suna samu ne kai-tsaye daga hannun Babban Bankin Najeriya, amma a yanzu sai dai su saya a kasuwar bayan-fage,” inji shi.

Dan kasuwar ya ce duk da cewa karin farashi da suke yi a bangarensu bai wuce na Naira 50 zuwa 200 ba, akasarin masu hulda da su gani suke yi tamkar daga wajensu matsalar take, inda ya ce sun rasa dimbin abokan hulda a sanadin matsalar.

“Wani misali kuma da zan ba ka, shi ne na man girki mai suna Power Oil da na sayi katan guda a kan Naira dubu 23 da 200. Na sayar a kan Naira dubu 23 da 600, ka ga a gaba daya ina da ribar Naira 400 ne.

“Amma da na koma kasuwa don sake sayo wani katan sai na samu ya koma Naira dubu 26 da 200, wato an yi karin Naira dubu uku, kuma duk a kasa da mako biyu,” inji shi.

Matsalar ta shafi manyan kantunan zamani

Rukunin kantunan Sahad da ke Abuja yana daya daga wurare da ake kayyade farashin kaya inda ake rubuta farashi a kan kowace kanta da take dauke da kayan sayarwa.

Malam Abdullahi Ibrahim Isa wanda shi ne Babban Manaja Mai Kula da Ma’aikatan Kantin na Tsakiyar Abuja (Central Area), ya ce matsalar ta samo asali ne daga bangarori da yawa kamar tashin farashin Dala da hana shigo da nau’o’in wasu kaya ko karin haraji, sai kuma karin kudin jirgi da sauran sassan sufuri.

Ya ce matsalar ta faro ne tun lokacin dokar kullen cutar coronavirus wadda ta tilasta raja’a a kan kamfanonin gida kawai.

Babban jami’in ya ce kamfaninsu da yake hulda da mabambanta hanyoyi uku wajen sayo kaya da suka hada da masana’antu kai-tsaye da masu dillancin kayan da kuma ’yan kasuwa, a kullum yana la’akari da hanya mafi sauki ce ta yin bincike kafin sayo kayan.

“A wani zubin idan muka tuntubi kamfani amma ya zamo babu kaya a kasa, sai mu je kasuwa saboda ba za mu zauna babu kaya a kasa ba.

“Sannan idan aka yi dace sai a samu tsohon kaya ne da su, sai mu samu a farashi mai sauki,” inji shi.

Ya ce hana shigo da shinkafa tare da tallafa wa manomanta da masu sana’anta ta, za su taimaka wa kasar nan ta fuskar samar da ayyuka da kuma dogaro da kai, inda ya bukaci gwamnati ta fadada lamarin a bangaren taimaka wa masu sana’anta sauran kayan masarufi a nan gida.

“Hakan zai magance idan wata sabuwar gwamnati ta zo, ba za ta bude iyaka kara-zube ba, wanda hakan ka iya mai da hannun agogo baya ta fuskar dogaro da kai ga kuma matsalar shigo da makamai da ake sa su a cikin kayan,” inji shi.

Ana cikin tsaka-mai-wuya

A Kano ma farashin kayan masarufi a kasuwanni kullum kara hauhawa yake yi, lamarin da ya sa talakawa suka shiga tsaka-mai-wuya.

A baya kayan masarufin sukan tashi ne a lokutan bubukuwa ko watan azumin Ramadan musamman kayayyakin da ake tsananin bukatar su.

A yanzu haka buhun fulawa wanda ake sayarwa wata uku da suka gabata a kan Niara dubu 16 ya koma Naira dubu 20. Haka man girki da ake sayarwa a kan Naira dubu 19 ya koma Naira dubu 24.

Katan din magi da ake sayrwa a kan Naira dubu takwas ya koma Naira dubu 10. Sai shinkafa da ake sayarwa Naira dubu 16 ta koma Naira dubu 20. Haka taliya da ake sayarwa a kan Naira 4000 ta koma Naira 4500 zuwa sama da sauransu.

Tashin Dala

Wani dan kasuwa mai suna Alhaji Jamilu M. Ya’u da ke Kasuwar Singa, ya ce karyewar darajar Naira da tashin farashin Dalar Amurka ne ummul-haba’isin hauhawar farashin kayayyakin.

“Idan kin duba a kullum Dalar Amurka tana kara tashi wanda hakan yake shafar kayayyakin yau da kullum ba wai kawai kayayyakin da ake kawowa daga kasashen waje ba, hatta kayayyakin da ake sarrafawa a kasar nan.

“Abin da ya janyo hakan kuwa, saboda yawancin kayayyakin da masu kamfanonin suke amfani da su ana sayo su ne daga kasashen waje.

“Ko shinkafar gida da kike gani, injunan da ake amfani da su ana sayo su ne daga kasashen waje, don haka tsadar kayan ke karuwa a kullum,” inji shi.

Rashin wutar lantarki

Har ila yau ya ce rashin wutar lantarki ya kara sa farashin kayayyakin suna karuwa a kullum.

“A kullum masu masana’antu suna gudanar da ayyukansu ta amfani da man dizal da fetur, to yaya za a yi kayayyaki ba za su tashi ba? Dole masu masana’antu su biya ma’aikata su fitar da kudin dizal da sauransu. Haka suna biyan masu kula da injunan wadanda ba ’yan kasar nan ba ne,” inji shi.

Yawan haraji

Wani dan kasuwa mai suna Muhammad Sani ya ce yawan harajin da gwamnatoci ke dora wa ’yan kasuwa ne ke sanya farashin kayayyakin hauhawa.

Ya ce, “Babbar matsalar da take janyo hauhawar farashin kayayyaki ita ce ta haraji da gwamnatoci ke tatsa daga wurin masu kamfanoni da ’yan kasuwa.

“A yanzu harajin da dan kasuwa yake biya yana da yawa. Akwai wani haraji da a baya guda daya ne, amma a yanzu an raba shi kashi biyar. To duk wannan sai dan kasuwa ya fitar a kan kayan da yake sayarwa ya samu riba.

“To su kuma masu kamfanoni suna da burin da suke son cim-mawa ko ta halin kaka; Don haka suke fitar da kudin a kan kayayyakin da suke sayarwa.”

Wani dan kasuwa mai suna Muhammad Isma’il ya ce matsalar hauhawar farashin kayan masarufi tana da alaka da yanayin karbar haraji da gwamnatoci a matakai daban-daban suke yi daga ’yan kasuwa.

“A yanzu harajin da ake karba daga ’yan kasuwa ya ninka kusan sau biyar sannan harajin da gwamnati ba ta karba, yanzu ta dawo karbar sa.

“Akwai wani haraji da ake dora wa masu gidan abinci amma wallahi yanzu an sa shi a harajin da ’yan kasuwa suke biya,” inji shi.

Ya ce tashin farashin kayayyakin ya sa ’yan kasuwar sun shiga halin kaka-ni-ka-yi saboda abin ya shafi kasuwancinsu kai-tsaye.

Ya ce, “Tashin farashin kayayyakin fa ya shafi mu ’yan kasuwa domin ya taba jarinmu. Kullum idan dan kasuwa ya sayar da kayansa idan ya koma wajen da yake sayowa sai ya ji farashi ya hau, dole sai mutum ya nemo wasu kudin ya yi ciko, sannan zai iya saya.

“A takaice kullum shagon dan kasuwa ramewa yake yi saboda rashin kaya. Kayan da yake iya saye a da, su cika masa shago yanzu ba zai iya saya da jarin nasa ba. Wannan abu ba karamin damun mu yake yi ba.”

‘Lamarin sai addu’a’

Aminiya ta tattauna da wani dan kasuwa da ya zo Kasuwar Singa don sarin kayayyaki mai suna Gambo Rijiyar Zaki inda ya ce lamarin hauhawar farashin kayayyakin ya kai matakin da sai dai a yi addu’a kawai.

“Babu ranar da zan zo kasuwar nan ban samu karin farashin kayayyaki ba. Kari kuma na rashin tausayi, sai dai kawai a yi addu’a,” inji shi.

A cewar Gambo Rijiyar Zaki abin da ya fi damun sa shi ne yadda suke samun matsala da masu sayen kaya daga wurinsu wadanda yawancinsu talakawa ne.

“Kasancewarmu masu sayar da kayayyaki ga mutane a unguwanni muna fuskantar matsala a tsakaninmu da su, wadanda yawancinmsu talakawa ne.

“Idan ka gaya wa mutum farashin kaya zai ce maka jiya ba haka ya saya ba, don me za a yi masa kari? ’Yan kadan ne suke fahimtarmu, amma wallahi ba karamar wahala muke sha ba.

“Baya ga masu karbar bashi da muke fama da su wadanda ba su iya biya.

“Ya zama cewa a kullum mutum zai je kasuwa sai ya nemi wani jarin da zai sayo kaya.

“Nan ga farashin kaya da suke hawa, a gefe guda kuma ga kudin mutum a hannun ’yan bashi sun kasa fitowa. Wannan abu sai addu’a kawai,” inji shi.