✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 6 a Zamfara

Tukin ganganci ne ya haddasa hatsarin kamar yadaa kwamandan FRSC ya bayyana.

Akalla mutum shida ne suka rasu, sannan wasu shida suka ji rauni sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da su a kauyen Tazame a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara, a ranar Alhamis.

An rawaito cewa motar fasinjar kirar Sharon ta yi taho-mu-gama ne da wata mota.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Zamfara, Mista Iron Danladi ya shaida wa Kamfanin Dillacin Labaran Najeriya (NAN) cewa motar na kan hanyarta ta zuwa Sakkwato ne daga Abuja yayin da hatsarin ya afku.

Ya ce direban motar wanda ba shi da lasisin tuki, yana gudun ganganci ne  motar ta kwace sannan ta afka wa wata mota da ke tunkuro ta.

Danladi, ya kara da cewa wadanda suka ji rauni an kai su Asibitin Kwararru na Yariman Bakura da ke garin Gusau domin ba su kulawar da ta dace, sannan an ajiye gawar wadanda suka mutu a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin.