✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya yi ajalin mutum 13 a Ogun

Mutum 12 sun samu rauni a yayin hatsarin.

Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 12 suka jikkata sakamakon wani hatsarin mota da ya auku a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Wakilinmu ya rawaito yadda hatsarin ya faru tsakanin wata mota kirar Volvo marar rajista da wata motar haya kirar Mazda bas suka yi taho mu gama da misalin karfe 4 na yammacin ranar Laraba.

  1. Sakamakon gasar Firimiyar Najeriya a mako na 34
  2. ‘Abin da ya sa mijina ya kashe kansa’

Aminiya ta gano cewa motar hayar ta dauko fasinjoji fiye da kima inda take dauke da mutum 25 maimakon wurin zaman mutum 18 da aka tanadar.

Bayanai sun ce direban motar ya yi kokarin ketare wata mota ce da ke gabansa, lamarin da ya sanya motar ta kwace ta yi sukuwa kan wata mota da aka ajiye a bakin hanya.

Faruwar hakan ce ta sanya mutum tara suka mutu nan take, yayin da kuma hudu suka rasu bayan an garzaya da su asibiti.

Kakakin Hukumar Kiyaye Cunkoso da Kula Dokar Hanya (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da faruwar hatsarin yayin zanta wa da manema labarai a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun.

Akinbiyi ya bayyana cewa motar fasinjan na dauke da mutum 25 da suka hadar da maza tara, mata takwas da kuma kananan yara takwas.

A cewarsa, mutum 12 da suka ji rauni sun hadar da maza biyar, mata uku da kuma kananan yara hudu, sai kuma wadanda suka rasu da suka hada da maza hudu, mata biyar da kananan yara hudu.

“Motar hayar wacce ta fito daga Legas ta yi kokarin wuce wata mota ba da ke gabanta ta hannun da bai kamata ba.

“Hakan ya sanya ta sukuwa a kan wata mota da aka ajiye a bakin hanya, inda nan take mutum tara suka mutu.

“Ragowar hudun sun mutu a asibitin Idera, bayan ceto su da jami’an TRACE suka yi da jami’an Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa FRSC,” in ji sa.

Akinbiyi, ya kara da cewar wadanda suka ji raunin an kai su Asibitin Idera inda aka ba su agajin gaggawa.