✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin ‘Yan bindiga: Mazauna karkara sun gudu birni neman mafaka a Neja

Babu sauran wuri mai tsaro a gare mu.

‘Yan bindiga a Jihar Neja sun tilasta wa mazauna yankunan Mutun-Daya da Gunu da sauransu, tserewa neman mafaka a Minna, babban birnin jihar sakamakon samamen da suka kai yankin a safiyar Lahadi.

Rahotanni sun nuna cewa tazarar da ke tsakanin babban birnin da kuma yankunan da lamarin ya shafa, kimanin kilomita 20 ne kacal.

Wani mazaunin yankin mai suna Shehu Abubakar, ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun shigo yankin nasu ne tun da misalin karfe 5:20 na safiya a daidai lokacin da ake gabatar da Sallar Asuba.

Shehu ya ce maharan sun farmaki al’ummar Chibani da Kuchi da Injita da sauransu, inda suka yi ta cin karensu babu babbkaa har zuwa wurin karfe 11 na hantsi.

“Da alama sun biyo wasu shanu ne a yankin Mararaba Dandaudu saboda akwai manoma da ke kiwon shanu a yankin.

“Haka suka gudanar da harkokinsu hankali kwance a yankin Gwada da Sarkin-Pawa ba tare da fuskantar wata tirjiya ba. Lamarin sai kara tabarbarewa yake kullum,” in ji shi.

An ce daga bisani, maharan sun shiga kauyukan Mutun-Daya da Gunu wadanda ke kusa da garin Minna inda suka ci gaba da sheke ayarsu.

A cewar wani mazaunin yankin wanda ya bukaci a sakaya sunansa saboda dalilai na tsaro, “Babu sauran wuri mai tsaro a gare mu, galibin matanmu a Mutun-Daya suka samu mafaka sakamakon hare-haren da ‘yan bindigar suka kai mana a baya. Kuma daga Mutun-Daya zuwa Minna bai wuci tafiyar minti 20 ba.”

Harin ya jefa matafiya a yankunan cikin tsaka-mai-wuya bayan da aka samu labarin ‘yan ta’adda sun mamaye yankin.

Kauyen Mutun-Daya mahada ce mai muhimmanci wadda ta nan ne ake daukar hanya zuwa wasu sassan jihar, kamar Kuta da Zumba da Gwada da sauransu.

Ya zuwa hada wannan rahoton, an kasa samun Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Neja balle a ji ta bakinsa kan lamarin.