✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin kunar bakin wake ya kashe mutum 13 a Somalia

Tuni kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin.

Akalla mutane 13 suka mutu bayan da wani dan kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a wani gidan cin abinci da shaidu suka ce cike yake da jami’an gwamnatin da sauran ‘yan siyasa a yankin tsakiyar Kasar.

Gidan Rediyon Faransa na RFI ya ruwaito cewa, tuni kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakin kai harin, da ya jikkata wasu mutane 18, baya ga rayukan da ya lakume a garin Beledweyne da ke tsakiyar kasar Somaliya a ranar Asabar.

Cikin makonni biyun da suka gabata, sai da kungiyar ta Al Shebaab ta kai wasu hare-haren kashi biyu a sassan kasar Somalia.

Jami’an ‘yan sanda da na gwamnati sun tabbatar da harin kunar bakin waken da aka kai gidan cin abincin, amma ba su bayyana adadin wadanda suka mutu ba.