✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin caji ofis ya yi sanadin mutuwar dan sanda

Jami'im dan sanda daya ya rasa ransa a yayin harin.

Akalla mutum biyu ne suka mutu ciki har da jami’in dan sanda, a harin da bata-gari suka kai wani caji ofis a Jihar Ebonyi.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Loveth Odah, ta tabbatar da faruwar harin cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu.

“Da misalin karfe 12 na dare bata-gari kusan su 20 a cikin wata bas kirar Mitsubishi sun farmaki caji ofis din Ugbuodo, a Jihar Ebonyi, amma an ci karfinsu a yayin dauki ba dadin,” cewarta.

Ta cewa wasu daga cikin bata-garin sun kai wa caji ofis din farmaki ne ta baya inda suka shiga harbi kan mai uwa da wabi.

Loveth ta ce ’yan sandan sun yi nasarar bindige daya daga cikin maharan tare da kwato bindiga kirar AK47 guda daya a hannunsu.

Sai dai kuma an yi rashin sa’a wani jami’in dan sanda daya ya kwanta dama a yayin gumurzun.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jiahr, Aliyu Garba, ya ziyarci caji ofis din don gane wa idonsa irin barnar da aka yi.