✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Boko Haram: Babu wanda ya tsira a Borno

Tun da har Boko Haram ta kai wa gwamnan Borno hari to babu wanda ya tsira

Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi ya ce harin Boko Haram a kan Gwamna Babagana Zulum ya nuna babu aminci kuma babu wanda ya tsira a jihar.

A ziyararsa ta Babbar Sallah ga gwamnan, Shehun Borno ya nuna damuwa game da harin na ranar Laraba a hanyar gwamnan ta zuwa rabon abinci ga ’yan gudun hijira a Baga da ke Kudacin jihar.

“Idan har za a kai wa shugaban tsaron jiha hari, to wallahi babu wanda ya tsira saboda shi ne mafi girman matsayi kuma Babban Jami’in Tsaron jihar.

“Ina kara fada, idan har za a kai wa ayarin motocin babban mutum irinsa a jiha hari, to babu wanda ya tsira.

Shehun Borno, Alhaji Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi tare da Gwamna Zulum

“Abun sai kara lalacewa ya ke yi, saboda haka nake kara kira da mu daga hannu mu roki Allah Ya kawo mana dauki”, inji basaraken.

Gwamnan jihar wanda ya bayyana takaici da harin ya kalubalanci sojoji kan kasawarsu wajen magance hare-haren Boko Haram a jiharsa.

Rahotanni sun ce gwamnan ya ce idan har sojojin sun kasa, to shi zai yi amfani da mafarauta domin fatattakar mayakan kungiyar.

Game da annobar COVID-19, Shehun Borno ya yi kira ga ’yan jihar da su kiyaye dokoki da shawarwarin masana kiwon lafiya kan hanyoyin kariyar cutar.

Ya kuma bukaci gwamnan ya hanzarta daukar mataki kan yawan sare itatuwa a sassan jihar, musamman ta hanyar dashen itatuwa akai-akai, tun kafin a samu babbar matsalar muhalli sakamakon sare itatuwan.

Gwamnan ya yi godiya ga basaraken bisa ziyarar tare da bayyana shirinsa na magance matsaloin da Shehun na Borno ya koka a kai.