✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hare-haren Rasha sun tilasta wa mutum 100,000 gudun hijira

Hukumar ta kuma ce wasu dubbai sun tsallaka Romania da Maldova don neman mafaka.

Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi harsashen cewa ’yan kasar Ukraine sama da 100,000 ne suka gudu suka bar muhallansu sakamakon hare-haren da Rasha ta kaddamar a kasar.

Hukumar ta kuma ce akwai wasu dubbai sun tsallaka kasashe makwabta na Romania da Maldova don neman mafaka.

Rahotanni daga kasar dai na nuni da cewa tuni dakarun Rasha suka tunkari babbar birnin na Ukraine, Wato Kyiv gadan-gadan, kamar yadda wani babban jami’in tsaron Amurka ya tabbatar.

Jami’in wanda ya yi magana amma bai amince a bayyana sunansa ba ya ce ya zuwa yanzu, Rasha ta harba makami mai linzami sama da 160 a cikin Ukraine.

Tuni dai Shugaban Amurka, Joe Biden, ya bi sahun sauran takwarorinsa na kasashen Yamma wajen yin Allah wadai da matakin na Rasha, inda ya ce za su kakaba wa Rashar takunkumin karya tattalin arziki.

Shi kuwa a nasa bangaren, Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya sha alwashin ci gaba da kare kasarsa ko ana ha-maza-ha-mata.

Shugaban ya kuma yi kira ga ’yan kasar da su fito su yi fada, inda ya ce za a bayar da makami ga dukkan wanda yake sha’awar fafatawa.