Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa a cikin wannan fili da fatan Allah Ya amfanar da mu dukan bayanan da za su zo cikinsa, amin. Ga ci gaban bayani kan hanyoyin tafiyar da Gamin-Gambizar Sha’awa daga inda muka tsaya a makon jiya, da fatan Allah Ya isar da wannan bayani ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Hanya ta 6: Kula da Masarrafin Sha’awa:
Masarrafin sha’awa shi ne abinci! Abincin da muke ci na taka muhimmiyar rawa wajen inganta ko nakasa sha’awar dan Adam. Yanayin rayuwarmu ya sa abincin duk da aka samu sawa ake a ciki, hatta wadanda suka san illolin wasu abincin, sai kawai su kawar da kai su ci abincin da suka san yana da illa ga lafiyar sha’awarsu da jikinsu don dadinsa ko don nauyin bukatarsu a lokacin. Yana da kyau dan Adam a koyaushe ya kasance mai kiyayewa da kula da irin abin da zai saka a cikinsa, domin dadin abinci ba a baki ne kawai ba, amfani ko illar da zai yi yayin da aka sarrafa shi ya shiga cikin jini shi ne abin la’akari. Yawanci kayan dadin wannan zamani, wadanda ake ganin cin su gayancewa ne ba abin da suke haifarwa ga sha’awar dan Adam sai nakasu haka kuma ga lafiyar jikinsa gaba daya.
Nau’in abincin da ke nakasa Ma’aikatar Sha’awa:
*Nau’o’in abinci masu illa ga sha’awar dan Adam sun hada da duk wani abinci mai dauke da sinadarin caffein irin su nescafe da shayi da goro da lemun kwalba da sauransu, domin wannan sinadarin yana rage sarrafa sinadarin cortisol wanda ke da nasaba wajen habbaka aikin sinadaran sha’awa da kuzarin jiki.
* Sai nau’o’in abinci masu dauke da sinadarin cholesterol, irin su duk wani soyayyen abinci da jan nama da abincin kamfani da abincin gwangwani da sauransu. Shi wannan sinadari a kan ajiye shi ne a matsayin kitse a hanyoyin jini, wanda yakan rage karfin gudanar jini har a jijiyoyin al’aura, wanda sai jinin ya malala cikinsu ne kafin sha’awa ta hauhawa.
Nau’in abinci da ke gyara Ma’aikatar Sha’awa:
Kowane nau’in abinci akwai wani bangare na ibadar auren da zai habaka, wani zai sanya nishadi da jin dadi cikin zuciya da ma’aikatar hankali, wani na taimakawa wajen malalar jini cikin jijiyoyin ibadar auren, wani kuma kara yawan sinadaran sha’awa cikin jini ko inganta masarrafar da ke sarrafasu cikin jiki.
Motsuwar sha’awa da jin dandanonta da cimma biyan bukatar sha’awa ba su tabbata sai an samu abubuwan nan guda uku suna aiki daidai:
1. Ya kasance akwai wadatuwar sinadaran sha’awa cikin jini;
2. Ya kasance jini na malala da gudana sosai cikin jiki;
3. Sannan kuma ya kasance zuciya da ruhi da ma’aikatar hankalin mutum na cikin nishadi da wadatar zuci.
Idan daya ya samu nakasu cikin wadannan ukun, to ibadar aure za ta zama mai rauni koma ta ki yiwuwa gaba daya. Su kuma abubuwan nan uku da na zana ba su tabbatuwa sai da cikakkiyar lafiyar jiki, shi ya sa duk wani abinci mai inganta lafiyar jiki to tabbas zai inganta lafiyar sha’awa kuma, domin dai gaba daya sassan jikin dan Adam na aikin taimakanni-in-taimake ka ne, duk abin da ya shafi wani bangare na jiki zai yi tasiri ga kusan duk illahirin jiki. Don haka mu gane cewa cin abinci masu kara lafiya shi ne wayewa ba cin abincin gaye-gaye, irin na zamani ba, abubuwan kara lafiya kuwa ba kamar irin ganyayyaki da kayan marmari da ’ya’yan itatuwa. Akwai mamaki yadda wadansu ’yan gayun ke ganin cin ire-iren ganyayyakinmu na al’ada, kamar su zogale a matsayin kauyanci. Su Turawa asalin gayun, na kashe kudi masu yawa wajen kai su kasashensu suna amfani da su don sun san darajarsu wajen inganta lafiyar jiki da kiyaye jiki daga kamuwa da cututtuka. Cin nau’o’in ganyayyaki da ’ya’yan itatuwa da ’yan kauye ke yawan yi na daga cikin abin da ya sa suka fi na birni lafiya mai armashi, kuma shi ya sa da wuya ka ga mutumin kauye da katon ciki kamar an kifa tukunya, duk kayan dadin nan da dan birni ke ci, su ke sa masa wannan katon ciki, wadansunmu na ganin katon cikin nan albarka ce, yaya za a yi abin da ya canja maka siffarka ta asali ya taba zama albarka? Sayyidina Umar (RA) ya kira irin wannan cikin da “Mafi bala’in ciki.”
Ina kira ga ma’aurata su guji yawancin magungunan karin sha’awa na zamanin nan, domin komai dadin da aka ji wajen amfani da su, illar da suke haifarwa daga baya na sa a ji da ma ba a yi amfani da su ba. Yawancinsu kuma suna dauke da gurbatattun sinadaran nan na carcinogens, masu sa cutar daji (cancer).
Dukan abincin nan da zan jero, cin su a kai-a-kai ne kadai ke tabbatar da samun lafiyayyar sha’awa, ba wai a ce sai lokacin da aka so ne kadai za a ci su ba, amfaninsu kamar shan ruwa ne, don ka sha yanzu bai hana anjima ka sake jin kishin ruwa, don haka maigida sai ya dage da sayo su, ke kuma uwargida sai ki dage da saka su cikin duk girke-girkenku daidai misali. Sannan a lura, ba a son a cika musu wuta wajen dafuwa domin sinadaran ciki duk sai su kone, kuma su ne ke gina sha’awa ba wai dusar abincin ba. Da fatan Allah Ya sa a dace amin.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatar Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.