A ranar Litinin mai zuwa 4 ga Fabrairu ake bikin tunawa da Ranar Yaki da Cututtukan Daji ta Duniya. A kowace shekara hukumomin lafiya a duniya kan ware irin wannan rana domin fadakarwa kan hanyoyin kariya daga cututtukan daji. A yau za mu tunatar a kan wasu daga cikin hanyoyin da akan bi a kiyaye cututtukan daji.
Abin da masana suka gano wadanda idan aka kiyaye za su iya kare mu daga sharrin cututtukan daji sun hada da:
Barin amfani da taba sigari, wadda ban da sankarar huhu takan iya kawo sankarar mafitsara da ta hanji da ta makogaro.
Barin amfani da barasa, wato giya, wadda kan iya jawo kansa a hanta da hanji da huhu da koda da mama
Killace kai ga mata. An yi amanna ciwon kansa na bakin mahaifa ya fi kama mata masu zaman kansu da mata masu yawan auri-saki, saboda su suka fi hadarin kamuwa da kwayar cutar birus ta human papilloma, mai sa kansar bakin mahaifa.
Allurar rigakafi kan taimaka wajen kiyaye wasu nau’o’i na kansa. Akan iya kiyaye kamuwa da kansar hanta wadda kwayar cutar birus ta hepatitis B, ke kawowa idan aka yi wa mutum allurar rigakafinta. Dukan ma’aikatan lafiya wadanda su ne suka fi shiga hadarin kamuwa, akan so su karbe ta. Sai kuma jariran da mahaifansu ke dauke da kwayar cutar hepatitis din, su ma yana da kyau da zarar an haife su a kai su a yi musu. A yanzu ana samun wannan allura a asibitocinmu kuma an sa ta a jadawalin allurar rigakafi na kasa baki daya, ta yadda kusan duk jaririn da aka haifa aka kai allura, sai an yi masa.
Kiyaye yara daga yawan cizon sauro. An tabbatar da cewa wani irin ciwon daji na kumatu Burkittlymphoma a yara yana daya daga cikin cututtukan da yawan cizon sauro ke kawowa. Don haka yawan sa yara cikin gidan sauro da dare zai taimaka matuka.
Sai yawan rage shiga rana wanda kan iya kiyaye kansa ta fata, musamman ga mutane masu hasken fata kamar zabiya.
Rage kiba. Masana sun tabbatar da cewa masu kiba sosai suna cikin hadarin kamuwa da ciwon sankara, musamman idan wani a danginsu ya taba yin ciwon. Don haka sai a rage maiko a abinci, a rika kara ganyaye da kayan itatuwa. Sai kuma a hada da yawan motsa jiki
Binciken masana a dukan sassan duniya ya tabbatar da cewa yawan shan koren shayi wato green tea kan iya rage hadarin kamuwa da ciwon dajin kowane sashe na jiki, domin shi koren ganyen yana da sinadarai masu yawon neman irin wadannan kwayoyin da suka bijire suke zama kansa, kuma su yi maganinsu.
Dukan wadanda suka ba shekara hamsin baya kuma maza ne ko mata, yana da kyau duk bayan shekara biyu su rika zuwa tantance cututtukan daji na hanji ta hanyar gwajin bayan gida, wanda yanzu akwai a asibitoci musamman na kudi. Mata kuma da suka haura hamsin yana da kyau su rika zuwa awon tantance cututtukan daji na mama da na bakin mahaifa. Wannan ya zama wajibi ga wadanda za su iya domin idan aka gano daji da wuri, an fi iya maganinsa. Idan aka gano ciwon daji a kurarren lokaci, maganinsa sai an sha wahala.
Da fatan Allah Ya kare mu baki daya.
Amsoshin Tambayoyi
Bayan ciwon kanjamau akwai ciwon da zai kama mutum a yi masa awon jini na CD4?
Daga Sulaiman Potiskum
Amsa: Eh, ana iya wannan awon a ciwon daji na kwayoyin jini wato sankarar jini. A sankarar jini wannan gwaji lambobin kwayoyin CD4 na nuna sun yin sama, a ciwon kanjamau kuma suna nuna kwayoyin CD4 sun yi kasa.
Kiba ta dame ni, na dauki matakin guje-guje da rage cin abinci amma sai karuwa nake. Wadanne matakai ya kamata in kara a kai?
Daga Aminu D.
Amsa: Watakila akwai inda kake yin wasu abubuwan ba daidai ba, misali watakila abincin ne ba a rage masa nauyi ba wato wani nauyi da muke aunawa a ma’aunin calory. Idan ka rage amma maimakon sau uku a rana kana ci sau shida ai ka ga ba ka yi ragi ba kari ka yi, ko idan ba ka rage maiko ba misali shi ma nauyin abincin ba zai ragu ba. A inda ka ce kana gudu kuma zai yi wahala ka rika iya gudu na minti 20 zuwa 30 a rana. Don haka ba dole sai gudu ba, ka dauki abin da za ka iya jurewa, kamar tafiyar sassarfa, ko kwallon tennis ko dai wani abu da kai a ra’ayin kanka kana jin dadin yin sa kuma za ka iya shi a kullum
Da gaske ne yawan shan ruwa kan sa suma saurin tofowa?
Daga Saminu Yelwan Shendam
Amsa:A’a ba yawan shan ruwa ba ne ya fi sa suma saurin fitowa, cin abinci mai lafiya hadadde wato balanced diet, wanda ruwa ma na daga ciki, shi ne ke sa suma saurin fitowa ta fito lafiyayiyya mai sheki ba mai yawan gutsurewa ba.
Shin shaken ganyen zogale yana da wani amfani ko akasin haka?
Daga Idris Keffi
Amsa: A’a shaken ko ma mene ne ta hanci in dai ba likita ne ya ba da shi ba akwai hadari sosai.
Me ke sa ciwon kai a gefen kai kusa da ido kuma mene ne maganinsa?
Daga Maman Ummi, Kaduna
Amsa:Ciwon kai irin wannan a likitance zai iya zama dayan uku, tunda kin ce yana zuwa har kusa da ido, zai iya zama na migraine ko na matsalar murar sinusitis ko na irin wanda muke kira cluster wanda ya fi kama masu yawan aiki ba gajiya da ’yan sigari ko masu yawan shan barasa. Dukansu dai suna shige da juna amma idan kika je likita ya duba ki zai iya tantance ko wane ne ya ba ki magani, domin wasu lokuta ko an sha magungunan kashe radadi irin su parasitamal ba sa dainawa.