✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hanyoyi 7 da za a bi domin magance sanko

Mutane da dama ba su sha’awar sanko a kansu kuma hakan yakan shafi namiji ko mace. Sanko abu ne wanda ke matukar bata kyawun mutum…

Mutane da dama ba su sha’awar sanko a kansu kuma hakan yakan shafi namiji ko mace.

Sanko abu ne wanda ke matukar bata kyawun mutum kuma tabbas sanko na da sababi daga jinsin mutum.

Idan har akwai mai sanko a dangin mutum zai iya kamuwa da shi ko kuma a haife shi da shi.

Sannan akwai wasu abubuwa da suke janyo samun sanko, kamar yawan gajiya ko yawan amfani da launi a gashi domin rage furfura da sauransu.

A yau Aminiya ta kawo muku wasu hanyoyin da za a bi domin magance wadannan matsaloli.

  • A samu man ‘Castor’ da  man kwakwa a hada su wuri daya sannan a rika shafawa a fatar kai, a rufe kan da leda na tsawon minti biyar. Yana da kyau a yawaita yin haka don samar da gashi a sankon.
  • A yawaita amfani da ruwan ganyen dogon yaro domin yana tsiro da gashi da wuri kuma yana hana furfura a gashi. A tafasa ganyen dogon yaron idan ya huce sai a rika wanke kai da ruwansa.
  • Ruwan na’a-na’a da ruwan ‘Aloe Vera’ na dauke da sinadaran bitamin A da E da kuma C, yana kuma taimakawa wajen fitar da gashin da ya zube da wuri. A rika hada ruwan na’a-na’a da ruwan Aloe Vera kadan sai a rika sha na tsawon mako biyu za a ga canji.
  • Cin albasa na taimakawa wajen feso da gashi. Yana da kyau a yawaita cin danyar albasa kamar guda biyu a rana. Za a iya yin kwadonta da rama ko da latas domin saukin ci. Sannan a yawaita jajjaga ta ana shafawa a inda sankon yake za ta taimaka.
  • Gwaiduwar kwai da ruwan lemun tsami da kuma man zaitun na taimakawa wajen fitar gashi da wuri. A same su sannan a haxa su waje daya sannan a shafa a fatar kan. Yana da kyau a riqa yin wannan kamar sau biyu a mako.
  • A samu ‘Baking Soda’ da kuma man wanke kai a rika shafawa a sankon, yin haka na magance kowace matsalar fata hade da na amosanin ka sannan yana taimakawa wajen haifar da gashin kai.
  • Lalle da kuma man kwakwa a hada su a wuri daya sannan a shafa a kan sankon na tsawon minti 30 suna taimakawa wajen magance matsalar sanko da rashin gashi.