✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hamza Al-Mustapha ya kai wa Wike ziyara a Fatakwal

Ya kai ziyarar ce a Fatakwal ranar Litinin

Dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar AA, kuma tsohon babban dogarin tsohon Shugaban Najeriya Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha, ya kai wa Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike Ziyara.

Dan takarar ya ziyarci Gwamnan ne a fadar gwamnatin jihar da ke Fatakwal, babban birnin jihar a ranar Litinin.

Al-Mustapha ya isa gaidan gwamnatin ne wajen misalin karfe 4:30 na yamma, kafin daga bisani ya shiga wata tattaunawar sirri da Gwamnan.

Dan takarar, wanda ya isa Fatakwal da tawagarsa ya kai ziyarar ce a wani bangare na neman goyon bayan da yake yi gabanin babban zaben 2023 da ke tafe.

A ’yan kwanakin nan dai, Gwamna Wike ya sha karbar bakuncin ’yan takara daga jam’iyyu daban-daban, duk kuwa da kasancewarsa dan jam’iyyar PDP.

Sai dai alamu na nuna cewa akwai baraka tsakaninsa da sauran jagororin jam’iyyar, musamman ma dan takararta na Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, da Shugabanta na kasa, Iyorchia Ayu.